Da dumi-dumi: Bayan janye masa, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe zaben fidda gwanin PDP

Da dumi-dumi: Bayan janye masa, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe zaben fidda gwanin PDP

Gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki ya lashe zaben fiddan gwanin dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Jam'iyyar ta bayyana hakan da yammacin Alhamis bayan kammala zaben a babban filin kwallon Samuel Ogbemudia, Benin City, babbar birnin jihar Edo.

A filin zaben da ya gudana yau, an samu halartar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da sauran manyan jam'ian jam'iyyar.

Hadimin gwamna Obaseki kan Soshiyal Midiya, Jack Obinyan, ya bayyana hakan a shainfa na Tuwita.

Yace: " Ko da baka samu labari ba, gwamna Obaseki ya lashe zaben ba tare da fuskantar wani kalubale ba, shi kadai ne dan takarar PDP."

"Za'a gudanar da zaben ranar 19 ga Satumba, 2020."

Da dumi-dumi: Dukkan yan takara sun janyewa gwamna Godwin Obaseki a zaben fidda gwanin PDP
Godwin Obaseki a zaben fidda gwanin PDP
Asali: Twitter

Godwin Obaseki ya samu wannan nasara ne bayan dukkan abokan takararsa sun janye masa duk da cewa shi ne na karshen da aka tantance cikinsu.

Da farko, Gideon Ikhine, ne ya fara janyesa masa, sannan Omoregie Ogbeide-Ihama wanda ya shiga kotu a baya domin a hana Obaseki takara amma ya janye daga karshe.

Na karshe shine Kenneth Imasuagbon wanda ya janye da safiya yau a filin zabe.

KU KARANTA: Tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, Abiola Ajimobi, ya mutu

Da dumi-dumi: Bayan janye masa, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe zaben fidda gwanin PDP
Da dumi-dumi: Bayan janye masa, Gwamna Godwin Obaseki ya lashe zaben fidda gwanin PDP
Asali: Facebook

Yanzu za'a kara tsakanin Godwin Obaseki da jam'iyyar PDP da Osaze Ize-Iyamu na jam'iyyar APC. Wadannan yan takara biyu ne suka goga raini a shekarar 2016 kuma zasu sake yanzu.

Babban shine kawai sun sauya jam'iyyar, kamar yadda hoton dake sama ya nuna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel