Bidiyon taron NEC na APC da ke gudana a yanzu, Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyya sun hallara

Bidiyon taron NEC na APC da ke gudana a yanzu, Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyya sun hallara

An fara taron Majalisar zartarwa, NEC, ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar shugaban kasa na Aso Rock.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suna daga cikin wadanda suka hallarci taron.

Mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom ne ya kira taron.

Tuni dai shugaban kasa ya amince da Giadom a matsayin shugaban riko na jam'iyyar bayan da kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole.

DUBA WANNAN: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bude taron misalin karfe 12 na rana.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, Kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Femi Gbajabiamila da gwamnoni 15 suma sun hallarci taron.

Bidiyon taron NEC na APC da ke gudana a yanzu, Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyya sun hallara
Bidiyon taron NEC na APC da ke gudana a yanzu, Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyya sun hallara. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

Gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Nasarawa, Niger, Jigawa, Yobe, Plateau, Kogi, Imo, Gombe, Osun, Ogun, Lagos, Kwara, Ekiti, Kano da Kebbi.

Sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka samu hallartan taron sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, jagoran majalisa, Hassan Doguwa da mataimakin bulaliyar majalisar wakilai na tarayya, Rt. Hon. Nnenna Ukeje

Ga hotunan yadda taron ya kasance a nan kasa:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel