Jerin Abubuwa 6 da ka iya hanaka samun shiga sabon diban shirin N-Power

Jerin Abubuwa 6 da ka iya hanaka samun shiga sabon diban shirin N-Power

Ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa za'a sallami matasan N-Power da aka dauka a shekarar 2016 wannan watan na Yuni, 2020.

Hakazalika za'a sallami wadanda aka dauka a 2018 a watan Yuli, 2020.

Shirin N-Power ya dauki matasa 500,000; karon farko an debi mutane 200,000 a Satumba 2016, sannan 300,000 a watan Agustan, 2018.

Ma'aikatar ta ce za'a fara sabon dauka ne daga ranar Juma'a, 26 ga Yuli, 2020 kuma za'a dauki mutane 400,000.

Za'a bude shafin yanar gizon rijista daga ranar 26 ga Yuni, 2020 domin masu bukata su nema.

N-Power shiri ne da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar a shekarar 2016 karkashin ofishin jin dadin al'umma.

Jerin Abubuwa 6 da ka iya hanaka samun shiga sabon diban shirin N-Power
Shirin N-Power
Asali: UGC

Amma ga jerin abubuwa shida da zasu iya hana mutum samun shiga shirin:

1- Idan ka kasance kana cikin sahun waɗanda suke shirin N-Power na baya(Batch A and B), ko ka ƙara cikewa ba zaka yi nasarar kasancewa a sahun sababbin da za'a ɗauka ba.

2- Idan nambar BVN ɗinka bai yi daidai da sunan da kayi rigistar N-Power ba zaka samu damar shiga sahun sababbin waɗanda zasu ci gajiyar sabon shirin ba.

3- Idan kayi kuskure wajan saka nambar asusunka(account number) ko BVN. za'a hanaka shiga sabon shirin N-Power.

4- Sannan idan baka yi nasara a gwajin da za'a gudanar a yanar gizo-gizo (online test) ba, duk da kasancewa gwajin zai kasance mai sauƙi. A nan ma ba zaka samu nasarar shiga sabon shirin N-Power ba.

5- Idan kayi kuskure a wajan zaɓar matakin karatunka ko ajin da kake , ba zaka yi nasarar shiga sabon shirin N-Power ba. misali mai NCE dole ya cike NCE.

6. Idan kana amsan albashi da wata ma'aikatar gwamnati ko mai zaman kanta, ba za'a dauke ka ba saboda za'a iya ganowa daga lamban BVN.

Daga Mutawakkil Binji

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel