Hotuna da bidiyon motocin alfarma da ke garejin Kaftin Ahmed Musa
- Har a yau, Ahmed Musa na daya daga cikin 'yan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles masu nasara
- Dan wasan kwallon kafar ya yi wasa a Ingila, Netherlands, Rasha kafin ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudi Arabia
- Dan kwallon kafar da ya saka kwallo sau hudu a raga a yayin gasar kofin duniyar, ya bayyana garejinsa a yayin da yake buga kwallon tennis
Har a yau, Ahmed Musa na daya daga cikin 'yan kwallon kafa masu tarin nasara a Najeriya. Ba a Najeriya kadai ba, za mu iya cewa a duniya saboda irin bajintar da ya gwada a gasar kwallon kafa ta kofin duniya.
Dan wasan kungiyar Al Nassr ya jefa kwallo hudu a raga yayin wasan kwallon kafa na kofin duniya.
Amma kuma, nasarorinsa ba a wurin kwallon kafa suka tsaya ba inda yake taimakon kungiyarsa a gasa daban-daban.
Tsohon dan kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ya bayyana garejinsa ko ma'adanar motocinsa a kafar sada zumuntar zamani a yayin da yake kwallon tennis da wani.
A bidiyon da ya wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, an ga mota kirar Mercedes Benz GWagon wacce kudinta ya kai N120 miliyan tare da Range Rover Velar mai darajar N40 miliyan sai kuma Porsche Macan wacce kudinta zai kai wurin N30 miliyan.
KU KARANTA: An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca
Musa na daga cikin 'yan kungiyar kwallon kafa ta kasar nan da suka yi nasarar samun jinjina a kofin kasashen Afrika da aka yi a kasar Misra.
Dan shekaru 27 din ya zama kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya bayan fitar John Obi Mikel daga kungiyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng