Yanzu-yanzu: Bangaren Abiola Ajmobi sun yi watsi da taron NEC na APC

Yanzu-yanzu: Bangaren Abiola Ajmobi sun yi watsi da taron NEC na APC

Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar APC na bangaren Abiola Ajimobi, ya yi watsi da gayyatar da aka yi musu na taron shugabannin jam'iyyar.

Bayan taron kwamitin gudanar da ayyukan da ya dauka sa'o'i masu tarin yawa, NWC ta kara da cewa an hure wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunne ne sannan ya amince da taron.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, sakamakon tsanantar rikicin cikin gida a jam'iyyar APC, bangaren Victor Giadom ya kira taron shugabannin jam'iyyar na gaggawa a ranar Alhamis.

Za a yi taron ne ta yanar gizo a fadar shugaban kasa ta hanyar kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Za a bayyana wadanda ake so su halarci taron yayin da za a tura gayyatar yanar gizo ga wadanda za su halarci taron daga gida.

Karin bayani na tafe...

KU KARANTA: An kama sojan da ya yi wa Buratai da shugabannin tsaro kaca-kaca

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel