Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba

Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba

Wani dan Najeriya a kasar Indonesia yayin tsere wa jami'an hukumar kula da shige da fice na kasar ya daka tsalle daga gida bene na tara ya diro kasa kuma ya tsira da ransa.

A cewar rahoton da The Nation ta wallafa, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba a Gadin Nias, Jakarta da ke Indonesia.

Rahotanni ba su ambaci sunan mutumin ba da ake zargin yana kokarin tsere wa jami'an hukumar kula da shige da fice na kasar ne da suka zo gidan don kama mutanen da ba su da takardan izinin zama a kasar.

Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba
Bidiyon yadda wani dan Najeriya da ya diro daga bene hawa 9 kuma bai mutu ba
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump

Amma mutumin ya jikkata kuma an garzaya da shi zuwa wani asibiti da ke kusa.

Akwai wasu yan Najeriya a kasar ta Indonesia ta ce sa in sa da jami'an hukumar kula da shige da ficen saboda yawan barazana da suka musu tare da jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Kalli bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa kamar yadda wani Fasanmi Paul Abiola ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga a yammacin ranar Talata sun kai hari kauyen Karare da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina inda suka sace diyar dagajin kauyen, Ciroma Ahmadu Karare.

Mazauna kauyen sun ce 'yan bindigan sun sace matashiyar mai shekaru 20 tare da wata mata mai shekara 23 da ke da goyo a bayanta a lokaci da aka yi awon gaba da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yan bindigan da aka ce adadinsu ya kai 20 sun isa kauyen ne a kan babura dauke da bindigu kamar yadda suka saba.

Rahotanni sun ce sun bi gidaje da dama suna yi wa mutane fashi ciki har da gidan dagajin kauyen inda suka sace diyarsa.

Daya daga cikin mazauna kauyen, Mustapha Ruma ya ce yan bindigan sun kwace wayar dagajin kauyen sannan suka ba shi sabon layin waya.

Sun umurci ya kira su domin tattauna abinda zai biya domin fansar diyarsa.

Yan bindigan kuma sun sace wasu dabobi da kayan abinci daga wurin mazauna kauyen yayin harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel