Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump

Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump

Diyar shugaban kasa Donald Trump, Tiffany Trump da saurayinta Michael Boulus dan asalin kasar Lebanoon da Najeriya sun shirya angwancewa sakamakon karfin da soyayyarsu tayi.

Masoyan biyu sun saba wallafa kyawawan hotunansu a shafukansu na Instagram, Jaridar The Nation ta ruwaito.

A watan Disamban 2019, Tiffany mai shekaru 26 da Boulus mai shekaru 22, sun halarci wata liyafar gidauniyar Kuwait da America a ofishin jakadancin Kuwait da ke birnin Washington.

Sun karkace tare da daukar kyawawan hotuna tare inda suka wallafasu a shafukansu na Instagram.

Ko a lokacin da yayar Tiffany, Ivanka Trump ta wallafa hotunan 'ya'yan Trump da abokan rayuwarsu, Tiffany ta bayyana tare da Michael Boulus.

An haifa Tiffany Trump a shekarar 1993. Matar shugaban kasa Donald Trump ta biyu, Marla Maples ce ta haifeta.

Tiffany ce diya daya tak tsakanin mahaifiyarta da mahaifinta.

Tiffany bata dade da kammala karatunta na fannin shari'a ba daga jami'ar Georgetown da ke Washington D.C

Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta tsawatarwa PDP, INEC daga yunkurin hana Obaseki shiga zaben fidda dan takara

Ta hadu da Michael Boulus ne bayan da suka rabu da tsohon saurayinta.

Tiffany ta sanar da hakan ne yayin tabbatar da cewa tana soyayya da hamshakin biloniyan Najeriya Michael Boulus.

Boulos ya girma a jihar Legas a Najeriya inda danginsa ke da kadarorin biliyoyin daloli. Wannan ne yasa suka dace da diyar shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Masoyan biyu sun fara haduwa ne a kasar Girka inda suka je hutu a watan Yulin 2018. Kamar yadda al'amuran ke nunawa, soyayyarsu kullum kara karfi take yi.

Amma kuma, abinda har yanzu ba a sani ba shine, Shugaban kasa Donald Trump ya amince da soyayyar ko bai aminta ba.

Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Idan za mu tuna, shugaban kasa Donald Trump na amfani da kalaman kaskanci a kan Najeriya. Amma kuma duk da haka, yana ganin girman shugaban kasa Muhammadu Buhari duk da rashin ganin darajar kasar da yake.

Kamar yadda Pagesix ta bayyana, masoyin diyar shugaba Trump ya kai gaisuwa wurin 'yan uwanta.

Michael Boulus shine magajin Boulos Enterprises and SCOA Nigeria, kamfanin biliyoyin daloli da ya kware a kasuwanci daban-daban.

Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

An gano cewa Boulus Enterprises ya fara kafa tarihi a jihar Legas bayan da suka fara siyar da kayan karau na mata tare da wasu kananan abubuwan bukata.

A wurin 1950, Anthony da Gabriel sun fara fadada kasuwancin inda suka fara shigo da baburan Miele, Durkopp da Goricke. A 1959, sun fara shigo da baburan Suzuki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel