Coronavirus: Za a fara koyar da dalibai karatu ta gidajen rediyo talabijin a jihar Zamfara

Coronavirus: Za a fara koyar da dalibai karatu ta gidajen rediyo talabijin a jihar Zamfara

- Sakamakon rufe kafatanin makarantu a Najeriya, gwamnatin jihar Zamfara na shirin fara amfani da gudajen talabijin da rediyo wajen koyar da daliban

- Gwamnatin jihar ta yi bayanin cewa za a rika watsa darussan ne a dandalai daban-daban na sadarwa da kafofin watsa labarai

- A cewar shugaban SUBEB, wannan tsari na ilimantarwa zai taimakawa yara su ci gaba da karatunsu suna daga zaune a gida

A yayin da ake ci gaba da fama da annobar korona a duniya baki daya, gwamnatin jihar Zamfara ta fara shirin tsuro da wani sabon tsarin ilimantar da dalibai su na zaune a gida.

Gwamnatin Zamfara ta fara shirin amfani da gidajen rediyo da na talabijin wajen koyar da dalibai biyo bayan umarnin rufe kafatanin makarantu a Najeriya da aka yi saboda annobar korona.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, gwamnatin Zamfara za ta aiwatar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwar Hukumar samar da ilimin bai daya (SUBEB) da kuma ma'aikatar ilmin jihar.

Gwamnan jihar Zamfara; Muhammadu Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara; Muhammadu Bello Matawalle
Asali: UGC

Gwamnatin Zamfara ta ce ma'aikatar ilimi ta jihar da kuma Hukumar SUBEB, za su dauki nauyin shirin watsa darussan a gidajen rediyon jihar Zamfara da kuma gidan talabijin na NTA da ke Gusau.

Makasudin wannan tsari na ilmantarwa da gwamnatin jihar ta kawo shi ne, debewa yara kewa ta yadda za su yi riko da littattafansu a maimakon su zauna kurum su na zaman kashe wando.

Alhaji Abubakar Aliyu Maradun, shugaban hukumar SUBEB na jihar, ya ce manufar kawo wannan tsari na ilimantarwa shi ne taimakon yara su ci gaba da karatunsu suna daga zaune a gida.

KARANTA KUMA: Operation Hadarin Daji: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan daban daji a Katsina da Zamfara

Ya yi bayanin cewa, za a rika yada darussan ne a dandalai daban-daban na sadarwa da kafofin watsa labarai.

Yayin da ya ke bayyana matakin shirin, Maradun ya ce hukumar SUBEB ta kashe fiye da naira miliyan 5, kuma a shirye ta ke ta kashe abinda ya fi haka domin tabbatar da dalibai sun ci gaba da karatu a gida.

Alhaji Maradun ya ce wannan sabon tsarin karantawa da gwamnatin jihar ta kawo, zai ci gaba da kasancewa har bayan an bude makarantu, lamarin da ya ce hakan zai kara wa yara hazaka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel