Rikicin APC: Fayemi da Giadom sun ziyarci Buhari, basu samu ganinsa ba

Rikicin APC: Fayemi da Giadom sun ziyarci Buhari, basu samu ganinsa ba

Gwamnan jihar Ekitin, Kayode Fayemi da daya daga cikin masu ikirarin zama mukaddashin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Victor Giadom, suna ta kokarin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Su biyun sun ziyarci fadar shugaban kasa da ke Aso Villa a Abuja a ranar Talata amma basu samu ganin shugaban kasar ba.

Amma kuma sun samu ganin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Farfesa Ibrahim Gambari.

Idan za mu tuna, a ranar Talata Giadom ya mika wata takarda da ke kiran taron shugabannin jam'iyyar APC wanda ya ce za a yi a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.

Karin bayani na nan tafe...

KU KARANTA: Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel