Katsina: 'Yan bindiga sun sake kai hari, sunyi kisa sun kuma sace shanu 150

Katsina: 'Yan bindiga sun sake kai hari, sunyi kisa sun kuma sace shanu 150

'Yan bindiga a jihar Katsina sun sake kai hari kauyen Unguwar Ali mai nisan kilomita 10 daga Faskari a daren ranar Talata suka kashe mutum daya tare da sace shanu fiye da 150 a cewar mazauna garin.

Kamar yadda HumAngle ta ruwaito, miyagun da adadinsu ya fi 200 sun isa kauyen a kan babura misalin karfe 11 na dare inda suka rika bi gida-gida suna neman dabobi.

Wannan harin na zuwa ne mako guda bayan wasu matasa a Katsina sunyi zanga-zanga a kan hare-haren da ake kai wa garurruwansu wadda hakan ke janyo matsaloli daban-daban.

Katsina: 'Yan bindiga sun sake kai hari, sunyi kisa sun kuma sace shanu 150
Katsina: 'Yan bindiga sun sake kai hari, sunyi kisa sun kuma sace shanu 150. Hoto daga Humangle
Asali: UGC

Kauyen Unguwar Ali yana karkashin karamar hukumar Faskari ne a jihar ta Katsina kuma yana kan babban titin zuwa Sokoto daga Funtua.

Usman, wani mazaunin garin ya ce, "kamar dai yadda suka saba, sun iso kauyen mu a kan babura suna kirari daban-daban, adadinsu ya kai 200.

"Sun raba kansu, wasu sun tare babban titi yayin da wasu kuma suka bazu a cikin gari.

"Sun rika bi gidaje neman dabobi, sun sace min shanu shida da raguna biyu da nake noma da su. Bani da kudin sayen wasu, hakan zai shafi noman da na ke yi."

DUBA WANNAN: Yadda saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa don burge sabuwar budurwa

Wani mazaunin kauyen, Musa, ya ce 'yan bindigan sun harbe wani mutum daya da ya boye a cikin mota, sun shiga gidan mu da shagunan mu sun sace kayan abinci da wasu kayayyakin.

Ya ce kawo yanzu lissafin da mutane suka yi ya nuna cewa 'yan bindigan sun sace fiye da shanu 200, shi kansa sun saci nashi shanun biyar.

Isah, mazaunin Funtua kuma manomi a Unguwar Ali ya ce, " wannan abubuwan suna faruwa ne saboda wasu na amfana da hare haren nan."

Isah ya ce abinda kawai suke roko daga wurin gwamnati shine samar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

Ya ce, "Ana sace musu dabobi, mutane suna barin gonakin su. Na kashe fiye da N100,000 a gona ta amma dole na dena zuwa saboda tsoron harin yan bindiga."

Kawo yanzu dai Rundunar 'Yan sandan jihar Katsina ba ta ce komai ba game da harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel