Hotunan magidanci ya karairaya wata mata a kan ta hana shi dukan matarsa

Hotunan magidanci ya karairaya wata mata a kan ta hana shi dukan matarsa

Wata mata ta yi ikirarin cewa wani mutum da ya je dukan matarsa ya kakkarya mata hannu bayan yunkurin kwatar matarsa da tayi.

Mogbonjubola Awofolu ta wallafa hotunan hannunta da ya sha bandeji a shafinta na Instagram. Ta yi bayanin yaddawata mata ta kai mata ziyara amma sai mijin mai suna Tobi ya shigo tare da yunkurin dukan matarsa.

Mogbonjubola ta ce ita uwar dakin matar ce shiyasa ta shiga ciki. Mutumin ya lakada mata mugun duka tare da ikirarin cewa babu abinda za ta iya.

Ta yi bayanin cewa ta garzaya ofishin 'yan sanda da ke Ikorodu washe garin ranar amma sai ta tarar da mutumin yana hira da wasu 'yan sanda.

Bayan nan, ta yi ikirarin cewa ya kirata tare da tabbatar mata da cewa babu abinda zai faru koda tayi korafi.

Yadda magidanci ya karairaya makwabciya a kan hana shi dukan matarsa (Hotuna)
Yadda magidanci ya karairaya makwabciya a kan hana shi dukan matarsa (Hotuna). Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnoni 5 da suka yi kaca-kaca da mataimakansu, suka nakasa su a siyasance

Yadda magidanci ya karairaya makwabciya a kan hana shi dukan matarsa (Hotuna)
Yadda magidanci ya karairaya makwabciya a kan hana shi dukan matarsa (Hotuna). Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

Kamar yadda tace, "A ranar Juma'a. 19 ga watan Yunin 2020, wani magidanci mai suna Tobi ya zo dukan matarsa na hana shi.

"Ni ce uwar dakin matar amma ba wannan karon ne na farko da ya zo dukanta a gabana ba ko yaranta.

"Watanni biyu da aka kwashe ana dokar hana walwala, matarsa da 'ya'yansa na gidana. Ya ce tana masa tsageranci don haka ne yake son ladabtar da ita.

"Na sanar da shi cewa ba zai yuwu a yi hakan a gidana ba. Ba zai iya dukanta a gabana ba. Koda ya saba hakan ba zai yuwu ba.

"Kafin in san meke faruwa, ya dauka kujera tare da sanar mini da cewa idan na shiga zai yi min abinda bana so.

"Abu na gaba da na sani shine yadda ya buge ni na fadi na karya hannu. Duk da haka bai nuna nadamarsa ba don sai da ya kara min da duka da kafa.

"Mutanen da suka taru suna sanar da shi cewa ya duba yadda na fadi na samu rauni amma sai cewa yayi shi dan kungiyar asiri ne kuma zai iya kasheni.

"Na sanar da shi cewa za a kama shi kuma sai an bi min hakkina."

Ta kara da cewa, "Na samu an duba ni sannan na tafi ofishin 'yan sandan da ke Igbogbo. A nan na tarar da shi yana bai wa wata 'yar sanda mai suna Bukky cin hanci.

"Sun bukaceni da in rubuta abinda ya faru tare da bani wata takarda da zan kai asibiti.

"A lokacin da ya bar ofishin 'yan sandan, ya kirani a kan cewa ba za a bi min hakkina ba. Yanzu haka kwana uku kenan ina fama da karaya amma ya turo matarsa da N12,000 a kan cewa in je asibiti.

"Na sanar da ita cewa bana so, hakkina nake so a bibiyarmin a wurinsa".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel