Yanzu-yanzu: Godwin Obaseki ya samu nasara a kotu, an yi watsi da karar hanashi takara

Yanzu-yanzu: Godwin Obaseki ya samu nasara a kotu, an yi watsi da karar hanashi takara

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Fatakwal ta yi watsi da karar da daya daga cikin yan takaran kujeran gwamnan jihar Edo, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya shigar, TVC ta shaida.

Alkali Emmanuel Obile a ranar Laraba ya yi watsi da karar bayan dukkan bangarorin biyu suka yi sulhu tsakaninsu kuma wanda ya shigar da karar ya janye kararsa.

Mai baiwa jam'iyyar PDP shawara kan lamuran doka, Emmanuel Enoidem, ya bayyanawa manema labarai cewa janye karar da Omoregie Ogbeide-Ihama yayi ya sa Alkalin yayi watsi da karar.

Ya ce yanzu babu abinda zai hana gwamna Obaseki takara a zaben fidda gwanin da zai gudana gobe Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020.

Lauyan Obaseki, Alex Egesieme, ya tabbatar da haka.

Obaseki ya sauya sheka jam'iyyar PDP ne bayan kwamitin tantancewar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta ce bai cancanci takara karkashinta ba.

Daga bisani, shi da mataimakinsa Philip Shaibu suka sauya sheka PDP kuma aka basu daman takara kuma aka tantancesu.

Yanzu-yanzu: Godwin Obaseki ya samu nasara a kotu, an yi watsi da karar hanashi takara
Ihama - Wanda ya shigar da Obaseki kotu
Asali: UGC

A jiya mun kawo muku rahoton cewa babbar kotun tarayya dake zamanta a Port Harcourt, jihar Rivers ta dakatad da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, daga musharaka a zaben fidda gwanin dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daya daga cikin yan takara a jam'iyyar PDP, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya shigar da kara kotu cewa a hana gwamnan takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar.

A karar da ya shigar, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya ce yan takaran da suka sayi Fom kuma aka tantance lokacin da aka kayyade tun farko ya kamata a amince suyi musharaka a zaben fidda gwanin.

Hakazalika ya tuhumci sihhancin takardun karatun Obaseki; babban dalilin da ya sa jam'iyyar APC ta hana shi takara.

A shari'ar da ya yanke ranar Litinin, Alkali E.A Obile ya amince da bukatar Omoregie Ogbeide-Ihama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel