Rashin tsaro: Hukumar Soji ta tura jiragen yaki 5 jihar Katsina

Rashin tsaro: Hukumar Soji ta tura jiragen yaki 5 jihar Katsina

Babban hafsan Sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Baba Abubakar a ranar Talata ya bayyana cewa an tura karin jirage masu saukar angulu biyar jihar Katsina, rahoton Punch.

AM Abubakar ya ce an tura jiragen ne domin karfafa yaki da ta'addanci a jihar da kuma sauran jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayinda ya tafi yawon duba wuraren da ake gina titin jirgi a kauyen Bakuru domin sabon makarantar koyar da ilmin tukin jirgi.

Yace: "An tura karin jirage masu saukar Angulu da Alpha Jet tashar jirgin saman Umaru Musa ‘Yar’adua dake jihar Katsina."

"Wadannan jiragen sun hada da jirgi mai saukar Angulu Agusta 109 na leken asiri, na Jet-jet."

"Yanzu jimillan jiragen yaki 10 ake amfani da su wajen atisayen Wutan Daji, wani sashen Operation Hadarin Daji.”

Babban hafsan sojin saman ya jaddada jajircewan jam'iansa wajen dakile yan bindigan da suka addabi jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna.

"Hukumar Sojin sama za ta tsanantawa yan bindigan iya kai hare-hare Arewa maso yammacin kasa." Ya kara.

KU KARANTA: Bankin Duniya ta amince da baiwa Najeriya bashin $750m don inganta wutan lantarki

Rashin tsaro: Hukumar Soji ta tura jirage yaki 5 jihar Katsina
Rashin tsaro: Hukumar Soji ta tura jirage yaki 5 jihar Katsina
Asali: Depositphotos

Mun kawo muku rahoton cewa ranar Litinin 22 ga watan Yunin 2020 akalla mutum uku sun rasa rayukansu a wani hari da yan bindiga suka kai a wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Dandume a Jihar Katsina.

Yan bindigan sun kai hari kauyen Maikwama inda suka kashe mutum uku kafin suka saci shanu masu dimbin yawa kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Sun kuma sace kayan abinci.

Sun kai harin ne bayan kwana daya da kai hari wani kauye mai suna Kurmin Chakara inda suka yi garkuwa da wani Malam Kabiru.

Shugaba Buhari ya zajjara hafsoshin tsaro kan irin kashe-kashen da ake yi a mahaifarsa kuma ya jaddada musu cewa ba zai sake daukan wani uzuri daga garesu ba.

Hakazalika ya yi alhinin rashin hadin kai tsakaninsu wajen yaki da yan bindiga da yan Boko Haram a arewacin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel