Fadar shugaban kasa ta yi wa Gwamna Matawalle kiran gaggawa

Fadar shugaban kasa ta yi wa Gwamna Matawalle kiran gaggawa

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a ranar Talata ya yi bayanin inda ta kwana ga shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari a kan tsaron jiharsa.

Gwamnan ya ce cibiyoyin tsaro na kokarin ganin sun shawo kan matsalar 'yan bindiga da kuma rikicin jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kadan bayan tattaunawar sirrin da suka yi, Matawalle ya ce gwamnati ta tsananta tsaro domin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Ya ce: "Na samu ganawa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a kan al'amuran da suka addabi jihar Zamfara.

"Mun tattauna sosai a kan matsalar tsaron arewacin Najeriya ba wai jihar Zamfara kadai ba.

"Mun samu ganawa da mai bada shawara na musamman a kan tsaron kasa, gwamnonin arewa da kuma sifeta janar din 'yan sandan Najeriya.

"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ne ya gayyaceni kuma na yi mishi bayanin halin rashin tsaro da jihata take ciki. Mun kuma fahimci inda muka dosa.

"Gwamnatin jihar Zamfara tare da sauran cibiyoyin tsaro na iyakar kokarinsu wajen tabbatar da an shawo kan matsalar rashin tsaro."

Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ta yi wa Matawalle kiran gaggawa
Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ta yi wa Matawalle kiran gaggawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hadimin gwamna ya kona makwabtansa da ya yi mugun mafarki da su (Hotuna)

Kamar yadda gwamnan ya ce, gwamnatinsa na amfani da wani sabon salo wurin shawo kan matsalar 'yan bindigar.

Ana karbar tubabbun 'yan bindiga hannu bibbiyu tare da basu madafa yadda ba za su koma ruwa ba.

"Kun san a yayin shawo kan matsalar tsaro, dole ne a yi amfani da dabaru daban-daban. Tubabbun 'yan bindigar na matukar yi mana amfani don da su muke amfani wurin yakar wadanda suka ki tuba," yace.

Ya bada tabbaciin cewa ayyukan dakarun sojin kasar nan a jiharsa zai yi matukar yin amfani.

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya yi kira ga manyan hafsoshin soji da kwamandojinsa da su tashi tsaye don kawo karshen annobar rashin tsaro da ta addabi kasar nan.

Mukaddashin daraktan hulda da jama'a, Sagir Musa, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a kan abinda suka tattauna da Buratai tare da manyan hafsin sojin a ranar Litinin a Abuja.

Buratai ya ce taron an yi shi ne don janyo hankalin rundunar don yakar 'yan ta'addan Boko Haram da kuma 'yan bindiga da suka addabin yankin arewa maso yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel