Rashin tsaro: Lambar Gwamnan Zamfara ta fito a ofishin Hadimin Shugaban kasa

Rashin tsaro: Lambar Gwamnan Zamfara ta fito a ofishin Hadimin Shugaban kasa

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari, ya zauna da gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle a game da rashin tsaron da ake fama da shi.

Gwamnan ya bayyana cewa jami’an tsaro su na kokarin kawo zaman lafiya a jihar Zamfara.

Zamfara ta na fama da matsalar ‘yan bindiga da su ka addabi jama’a. Bello Matawalle ya bayyanawa ‘yan jarida jami’an tsaro sun dage wajen ganin an samu zaman lafiya.

Da ya ke jawabi bayan wannan ganawa a fadar shugaban kasa, gwamnan ya ce: “Na zo nan ne domin in hadu da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa kan lamarin tsaro.”

Gwamna Matawalle ya kara da cewa: “Ba a kan batun jihar Zamfara kawai ba, daukacin Arewacin Najeriya.

“Mun hadu a ofishin mai bada shawara kan harkokin tsaro tare da gwamnonin Arewa da Sufeta janar na ‘yan sanda da hukumomin tsaro. Mun yi doguwar magana a kan batun.”

KU KARANTA: APC: Buhari ya ba bangaren Giadom karfi a rikicin Jam'iyya

Rashin tsaro: Lambar Gwamnan Zamfara ta fito a ofishin Hadimin Shugaban kasa
Shugaban Ma'aikatan fadar Shugaban kasa Ibrahim Gambari Hoto: Aso Villa
Asali: Twitter

“Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ne ya gayyace ni in zo in yi masa bayanin halin rashin tsaro a jiha ta, wanda kuma na yi, haka mun fahimci inda mu ka dosa.” Inji sa.

“Gwamnatin Zamfara da sauran hukumomin tsaro su na bakin kokarinsu na maganin wannan matsala.”

A cewar gwamnan, su na yin duk abin da za ta iya domin mutane su samu zaman lafiya. “Akwai tubabbun miyagun da su ka ajiye makamai, aka yi sulhu da su; mu na aiki da su.”

“Wadanda ba su shiga yarjejeniyar sulhun ba, mu na fada da su.” Inji Mai girma gwamnan.

Matawalle ya na sa rai dakarun kasar za su ci nasarar ganin bayan ‘yan bindigan da ke Zamfara. “Jami’an tsaro su na kokari sosai, su na tare da mu na kusan wata guda kenan yanzu.”

Hukumar dillacin labarai watau NAN ta rahoto gwamnan ya na cewa: “Babu shakka sun samu nasarori sosai a aikin da su ke yi, dole kuma a cigaba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel