COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)

COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)

Duk da yawan wayar da kai tare da kashe makuden kudaden da gwamnatin tarayyar Najeriya ke yi a kan cutar korona, akwai wasu kauyuka a kasar da ba su san da wanzuwar cutar ba kwata-kwata.

Zokutu kauye ne da ke da nisan sa'o'i biyu daga garin Abuja. Sanannen abu ne idan aka ce kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da annobar na garin Abuja. Nan ne kenan cibiyar fitar da bayanai game da cutar.

Mazauna garin Zokutu sun ce basu taba koda jin labari ba a kan annobar da ta game duniya. Ba kuma su san ta yadda za ta iya shafarsu ba.

Tun a watan Fabrairun shekarar nan ne Najeriya ta samu mutum na farko da ke dauke da muguwar cutar. Tun daga wannan lokacin kuwa take ci gaba da yaduwa zuwa lungu da sakonnin kasar nan.

Hakazalika, alkalumman hukumar yaki da cutar a Najeriya ya tabbatar da cewa sama da mutum 20,000 ne aka tabattar da kamuwarsu da muguwar cutar.

COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)
COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna). Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Gwamnati na amfani da rediyo ko talabijin wurin bada bayanai tare da wayarwa jama'a da kai a kan cutar.

Sai dai kash! Kauyen Zokutu babu titin mota mai kyau, asibiti ballantana sauran hanyoyin sadarwa.

Hakazalika, babu wutar lantarki ballantana su kunna rediyo ko talabijin don sauraron labarai. Hakan ne yasa basu san da wannan cutar ba.

COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)
COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna). Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Rose Mishayi mazauniyar garin Zokutu ce. Ta ce basu taba samun labarin cutar ba. "Ba mu taba jin komai game da cutar korona ba. A yanzu haka bamu san yadda cutar za ta iya shafarmu ba.

"Mun dai ji cewa wata cuta ta shigo Najeriya amma bamu san komai game da ita ba," cewar Mishayi.

COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)
COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna). Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hadimin gwamna ya kona makwabtansa da ya yi mugun mafarki da su (Hotuna)

COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)
COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna). Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Ministan Buhari na yada labarai, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin Najeriya ta zuba kudi wurin bada sanarwa tare da wayar da kan 'yan kasa game da cutar.

Ya kara da cewa, wata kuri'ar jin ra'ayin mutane ta nuna cewa, kashi 99 na 'yan Najeriya sun ji labarin cutar.

Sai dai kuma kwamitin fadar shugaban kasa yace akwai bukatar jama'a yanzu su ji labarin cutar na musamman tunda ta fara shiga cikin al'umma sosai.

COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna)
COVID-19: Kauyen da basu san da wanzuwar korona ba a Abuja (Hotuna). Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel