Karin mutum 452 sun kamu da korona a Najeriya

Karin mutum 452 sun kamu da korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 452 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.3 na daren ranar Talata 23 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 452 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Karin mutum 452 sun kamu da korona a Najeriya
Karin mutum 452 sun kamu da korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-209

Oyo-67

Delta-37

Ogun-36

FCT-22

Abia-20

DUBA WANNAN: Hajj 2020: Sharruda 6 da Saudiyya ta gindaya kan Hajjin bana

Enugu-16

Bauchi-15

Kaduna-8

Ondo-8

Osun-7

Imo-3

Benue-3

Borno-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Talata 23 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 21371.

An sallami mutum 7338 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 533.

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohin arewa sun yanke hukuncin saka mafarauta da 'yan banga domin yakar matsalar 'yan bindiga da duk wani nau'in rashin tsaro da ke yankin.

Wannan ya biyo bayan yawaitar kashe-kashe a jihohin Katsina, Zamfara da sauran jihohin yankin, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Kungiyar gwamnonin arewa, wadanda suka yi taro ta yanar gizo don sake duba yanayin tsaron yankin, sun samu shugabancin Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong.

Gwamnan ya nuna damuwarsa da yadda rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a yankin wanda ya kai ga rashin rayuka da kadarori.

Gwamnonin sun yanke hukuncin kafa kwamitin da zai dinga lura da tsaron yankin wanda zai samu shugabancin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

Kwamitin ya kunshi gwamnan jihar Zamfara da na jihar Gombe a matsayin mambobi.

Kamar yadda wata takarda da daraktan yada labarai da hulda da jama'a na gwamna Lalong, Dr Makut Simon Macham ya fitar a Jos ta bayyana, ta ce gwamnonin sun shirya yakar matsalar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel