Kotu ta tsawatarwa PDP, INEC daga yunkurin hana Obaseki shiga zaben fidda dan takara

Kotu ta tsawatarwa PDP, INEC daga yunkurin hana Obaseki shiga zaben fidda dan takara

Wata babban kotu da ke zamanta a Ekpoma a jihar Edo ta ki amince da bukatar da aka gabatar a gabanta ne neman hana gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki neman takara a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP da za ayi ranar Alhamis.

Kotun ta haramtawa Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da jami'yyar Peoples Democratic Party (PDP) hana Obaseki da duk wani mai neman takarar da aka tantance shi daga shiga zaben da za ayi a ranar 25 ga watan Yunin 2020.

Wata kotun tarayya da ke Fatakwal a jihar Rivers, ta hana Obaseki shiga takara zaben fidda gwanin saboda karar da mai neman karar a PDP Omoregie Ogbeide-Ihama ya shigar.

Kotu ta taka PDP birki game da hana Obaseki shiga takarar zaben fitar da gwani
Kotu ta taka PDP birki game da hana Obaseki shiga takarar zaben fitar da gwani
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnonin arewa za su aika da mafarauta da 'yan banga su yaƙi 'yan bindiga

Omoregie Ogbeide-Ihama ya roki kotu ta hana Obaseki shiga takarar zaben fidda gwanin a kan cewa bai siya fom din takarar zaben ba a kan lokacin da jami'yyar ta kayyade a jadawalin yin zaben.

Ya roki kotun ta hallastawa masu neman takarar da suka siya fom dinsu a na neman takarar a cikin lokacin da aka kayyade a jadawalin zaben kawai.

Sai dai a wani bukatar da aka gabatarwa babban kotun Edo, wani Felix Irioh ya bukaci kotu ta kyalle Obaseki ya shiga a fafata dashi a takarar zaben fidda gwanin a kan cewa jami'yyar ta masa uzuri na musamman wato 'waiver'.

A yayin yanke hukuncinsa, Mai sharia J.O. Okeaya-Inneh ya ce, "A raayi na wadanda suka shigar da kara sun cika dukkan kaidojin bayar da umurnin abinda suke so kamar yadda ya faru a shariar Kotoye v CBN (1989), 1 NWLR PT. 98, 419 a 441.”

"Bayan cika kaidoji sun kuma gabatar da bukatarsu a kan lokaci saboda hakan yasa na ga ya dace in biya musu bukatarsu," in ji alkalin.

Amma duk da haka ya dage cigaba da sauraron shariar zuwa ranar 1 ga watan Yulin 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164