Gwamna so yake ya tsigeni daga kujera ta - Mataimakin gwamnan Ondo

Gwamna so yake ya tsigeni daga kujera ta - Mataimakin gwamnan Ondo

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi ya kawo kuka kan take-taken da gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, keyi na tsigeshi daga kujerarsa.

Gwamna Akeredolu da mataimakinsa Ajayi sun dade da shiga takun tsaka kuma hakan ya sabbaba sauya shekar mataimakin daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Mataimakin Ajayi ya koma PDP kuma ya lashi takobin fitowa takara a zaben da za ayi a watan Oktoba domin kayar da gwamnan.

Ajayi ya jaddada cewa ba zai yi murabus daga murabus ba amma gwamna Akeredolu na kokarin tsigesa ta bayan fagge.

Ya ce ana shirin tsigeshi ne ta hanyar baiwa kowani dan majalisar dokokin jihar N10m.

KU KARANTA: Kotu ta haramtawa Victor Giadom alakanta kansa da jam'iyyar APC

Gwamna so yake ya tsigeni daga kujera ta - Mataimakin gwamnan Ondo
Gwamna so yake ya tsigeni daga kujera ta - Mataimakin gwamnan Ondo
Asali: Twitter

A jawabin da sakataren yada labaransa, Babatope Okeowo, ya saki, ya ce yan sanda sun zagaye majalisar dokokin kuma duk ana hana duk dan majalisar da yaki amincewa da shirin shiga majalisa.

Jawabin yace: "Muna san a sani cewa mataimakin gwamna jajirtaccen dan siyasa ne, wanda shirye yake da duk wani irin tuggun da gajiyayyen gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu, yake yi."

"Don ya shiga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Agboola Ajayi bai aikata wani laifi ba."

"Muna masu bayyanawa cewa gwamnan da abokansa basu da isasshen adadi da rinyaje a majalisar dokokin jihar da zasu tsige mataimakin gwamnan da shi bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya."

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya sallami dukkan hadiman mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, bayan komawarsa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Hakan ya biyo bayan sallamar mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Allen Sowore.

Hadiman da wannan sallamar ya shafa sun hada da hadiminsa kan ayyuka na musamman, Olomu Bayo; hadiminsa mai daukan hotuna, Olawale Mukaila; mataimakin sakataren yada labaransa, Babatope Okeowo; hadimi na jiki, Samuel Ogunmusi.

Sauran sune Omotunmise Tokunbo; hadimin matar mataimakin gwamna, da Erifeyiwa Akinnugba, mai daukar hoton uwargidar mataimakin gwamna.

Amma mataimakin gwamnan ya mayar da dukkansu baki aikinsu kuma shi zai rika biyansu albashi da kansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel