Kungiyar kwadago ta dakatar da shiga yajin aiki kan ragewa ma'aikatan Kano albashi

Kungiyar kwadago ta dakatar da shiga yajin aiki kan ragewa ma'aikatan Kano albashi

- Kungiyar Kwadago reshen jihar Kano ta dakatar da yajin aikin da ta ke shirin shiga

- An cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar da kungiyar kwadogo kan batun zaftarewa ma'aikata albashi

- Gwamnatin Kano za ta mayar wa ma'aikatan Kano kashi 50% na albashinsu da ta cire

Bayan an samu maslaha da gwamnatin jihar Kano, kungiyar kwadago reshen jihar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin gargadi na mako daya da ta ke shirin shiga.

Kungiyar kwadago ta kudiri shiga yajin aikin na gargadi domin ta nuna rashin amincewarta a kan zaftare wani kaso na albashin ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi.

Sanarwar dakatar da yajin aikin ta fito ne daga bakin shugaban hukumar kwadago reshen jihar Kano, Kwamared Kabir Minjibir, yayin ganawa da kamfanin dilllancin labarai na kasa NAN.

Idan ba a manta ba, kungiyar kwadago reshen jihar, ta ba wa gwamnatin Kano wa'adin kwana 14 ta gaggauta dawo wa ma'aikatan gwamnatin jihar albashin su na watan Mayu da ta zaftare.

A yayin da wa'adin kwanaki 14 zai kare, kungiyar ta yi barazanar shiga yajin aiki na gargadi da jan kunnen gwamnatin jihar muddin ba ta warware hukuncin da ta dauka ba.

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Asali: UGC

Yayin da wa'adin kwanaki 14 da kungiyar ta bai wa gwamnatin jihar ya kare, ta kuma sake bata wa'adin kwanaki bakwai wanda zai fara daga karfe 12.00 na daren yau Talata, 23 ga watan Yuni.

Kwamared Minjibir yayin zantawa da manema labarai, ya ce su na sa ran za a cimma matsaya da gwamnatin bayan zaman da suka yi tare da ita a ranar Litinin.

"A yayin zaman karshe da muka yi da kwamitin gwamnatin wanda shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Usman Alhaji ya jagoranta, gwamnatin ta amince za ta mayar da kashi 50 cikin 100 na abin da ta cire daga albashin ma’aikatan."

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta ruwaito, gwamnatin jihar Kano ta musanta rahotannin da ke yaduwa na cewa tana yunkurin buɗewa ɗalibai makarantu a fadin jihar.

KARANTA KUMA: Gwamnonin Arewa sun gana da shugabannin tsaro na kasa

A baya bayan nan ne rahotanni kan shirin komawar ɗalibai makarantu a Kano sun yi ta gudana a kan harsunan mutane da dama.

Cikin 'yan kwanakin nan ne aka yi ta yada jita-jitar cewa, gwamnatin Kano ta kafa wani kwamiti domin duba yiwuwar buɗe makarantu duk da likafar annobar korona na ci gaba.

To sai dai a wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar ta bakin kakakinta, Malam Yusuf Aliyu ta bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege.

Sai dai wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta jihar ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, Yusuf Aliyu, ta bayyana labarin a matsayin tatsuniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel