Gwamnonin Arewa sun gana da shugabannin tsaro na kasa

Gwamnonin Arewa sun gana da shugabannin tsaro na kasa

A yayin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a yankin Arewacin kasar, gwamnoni 19 an yankin sun garzaya Abuja domin kai kukansu kan lamarin da ke ci musu tuwo a kwarya.

A ranar Litinin ne gwamnonin jihohi 19 na yankin suka gana da shugabannin tsaro na kasa a ofishin mai ba da shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara shi ne ya sanar da hakan bayan wata ganawar sirri tare da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

A makon jiya ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaro na kasa da su gana da gwamnnonin Arewa domin bijiro da matakan kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Gwamna Matawalle yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, ya ce gwamnatinsa tuni ta fara shimfida dabarun magance sha'anin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a jiharsa.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa
Asali: Twitter

Legit.ng ta fahimci cewa, a baya bayan nan ne 'yan daban daji, barayin shanu, da 'yan fashi da makami, suka sabunta ta'addanci musamman a jihohin Katsina, Neja da kuma Zamfara.

Ya yi bayanin cewa, 'yan ta'addan da suka tuba kuma suka rungumi zaman lafiya an maido su cikin al'umma, yayin da wadanda suka juya baya a kan hakan za su fuskanci fushin hukuma.

Yana mai cewa, "a yau mun gana da sufeto janar na 'yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro a ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa."

KARANTA KUMA: Jerin 'yan majalisar wakilai da suka fi kawo kudirorin samar da ci gaba a kasa

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Litinin, mutum uku sun rasa rayukansu a wani hari da 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka na karamar hukumar Dandume a Jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kai hari kauyen Maikwama inda suka kashe mutum uku sannan kuma sun yi awon gaba da shanu masu dimbin yawa kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Sun kai harin ne bayan kwana guda da kai hari kauyen Kurmin Chakara, inda suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Malam Kabiru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel