Da duminsa: Gwamnan Ondo ya sallami dukkan hadiman mataimakinsa

Da duminsa: Gwamnan Ondo ya sallami dukkan hadiman mataimakinsa

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya sallami dukkan hadiman mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, bayan komawarsa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), The Cable ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan sallamar mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Allen Sowore.

Gwamna Akeredolu da mataimakinsa Ajayi sun dade da shiga takun tsaka kuma hakan ya sabbaba sauya shekar mataimakin daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Mataimakin Ajayi ya koma PDP kuma ya lashi takobin fitowa takara a zaben da za ayi a watan Oktoba domin kayar da gwamnan.

Hadiman da wannan sallamar ya shafa sun hada da hadiminsa kan ayyuka na musamman, Olomu Bayo; hadiminsa mai daukan hotuna, Olawale Mukaila; mataimakin sakataren yada labaransa, Babatope Okeowo; hadimi na jiki, Samuel Ogunmusi.

Sauran sune Omotunmise Tokunbo; hadimin matar mataimakin gwamna, da Erifeyiwa Akinnugba, mai daukar hoton uwargidar mataimakin gwamna.

Sakataren yada labaran gwamnan wanda ya rattafa hannun kan jawabin, Sagun Ajiboye, ya umurci dukkan hadiman da aka ambata su sallamar da dukkan dukiyoyin gwamnati dake hannunsu ofishin shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin jihar.

Da duminsa: Gwamnan Ondo ya sallami dukkan hadiman mataimakinsa
Mataimakin gwamnan Ondo
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan sanda sun garkame hedkwatar jam'iyyar APC

A ranar Lahadi, mun kawo muku rahoton cewa an yi gajeruwar dirama a jihar Ondo daren Asabar yayinda kwamishanan yan sandan jihar, Bolaji Salami, ya hana mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, fita daga cikin gidan gwamnati.

Kwamishanan ya dakatad da mataimakin gwamnan ne tare da wasu hadimansa yayinda suke kwashe kayansu daga gidan gwamnatin bisa umurnin gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

A bidiyon da TheCable ta samu, ya nuna sai da suka kwashe sa'o'i suna mujadala amma yan sanda basu bari ya fita ba.

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin ya yanke shawarar sauya sheka jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin fito na fito da gwamnan a zabe.

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Allen Sowore, ya bayyanawa manema labarai cewa an tsare maigidansa na tsawon sa'o;i da dama, duk da cewa doka ta bashi kariya.

Amma hadimin gwamnan kan sabbin kafafen labarai, Richard Olatunde, ya ce an hana mataimakin gwamnan fita ne saboda yana kokarin kwashe wasu dukiyoyin gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel