Yanzu-yanzu: Yan sanda sun garkame hedkwatar jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun garkame hedkwatar jam'iyyar APC

Wasu jami'an yan sanda sun kulle hedkwatar uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bisa umurnin Sifeto Janar na hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu, The Nation ta ruwaito.

Hakazalika an samu labarin cewa IGP na yan sanda zai gana da bangarorin kwamitin gudanarwan jam'iyyar a hedkwatar hukumar misalin karfe 1 na rana.

An tattaro cewa kwamishanan yan sandan birnin tarayya ya umurci babban jami'in tsaron hedkwatar ya bayyanawa mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar cewa babu wanda aka amince ya shiga harabar hedkwatar.

Majiya daga cikin jam'iyyar ya bayyana cewa an kulle hedkwatar ne domin baiwa shugaban yan sandan damar duba umurnin da kotu tayi da kuma wanda za'a bi.

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun garkame hedkwatar jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Yan sanda sun garkame hedkwatar jam'iyyar APC
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan majalisar dokokin jihar Imo 13 sun kamu da cutar Coronavirus

Daga an amince wasu yan jarida su shiga da sharadin cewa ba zasu yi hira da kowani mutum dake cikin sakatariyan ba.

Dan sandan ya bayyana cewa: "Umurnin da aka bamu shine kada mu bari kowa ya shiga amma kun san tare muke aiki shi yasa muke nan."

"Babu hira da wani a nan yanzu. Ku samu labaranku a tsanake ku tafi."

Rikicin jam'iyyar APC ya dau sabon salo ne bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da dakatad da Adams Oshiomole matsayin shugaban uwar jam'iyyar.

Tun daga lokacin kwamitin gudanarwan jam'iyyar ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, a matsayin shugaban kungiyar na riko, amma mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom ya ce sam shine sahihin shugaban jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel