'Yan sanda sun damke 'yan KAROTA uku a Kano

'Yan sanda sun damke 'yan KAROTA uku a Kano

Rundunar Yan sandan jihar Kano ta kama jami'an Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Kano (KAROTA) uku a kan yi wa wani matashi mai suna Aminu Abdullahi duka.

Yan KAROTA sun yi wa Aminu dukka ne sakamakon rashin jituwa da ya yi sanadin karya wa matashin kafarsa kamar yadda Human Angle ta ruwaito.

Daga bisani dandazon matasa sun fara kai wa 'yan karotan hari kafin suka ceto Aminu daga hannunsu inda a halin yanzu yana samun kulawa a babban asibitin Murtala Mohammed da ke Kano.

'Yan sanda sun damke 'yan KAROTA uku a Kano
'Yan sanda sun damke 'yan KAROTA uku a Kano. Hoto daga Human Angle
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hira da ya yi da manema labarai a ranar Litinin a Kano.

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Ya ce ya samu rahoton afkuwar lamarin ne a yammacin ranar 19 ga watan Yuni inda ya kara da cewa lamarin ya faru ne a Ibrahim Taiwo Road da ke birnin Kano.

Mazauna garin Kano sun nuna damuwarsu kan rashin bayar da horo mai kyau ga 'yan KAROTA da suke ganin hakan ke janyo yawaitan rashin jituwa tsakaninsu da masu ababen hawa a jihar.

Akwai bukatar shugaban KAROTA, Dr Baffa Dan'agundi Ahmad ya bawa jami'ansa horo a kan hanyoyin da suka fi dacewa su rika hulda da al'umma a cewar wasu mazauna Kano.

Kakakin 'yan sandan ya ce 'yan sanda abokan kowa ne inda ya kara da cewa akwai alaka mai kyau tsakaninsu da sauran hukumomin tsaro.

Kazalika, ya bayyar da tabbacin cewa za ayi adalci a kan lamarin domin tabbatar da zaman lafiya tare da kiyaye afkuwar wani abu mai kama da wannan a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel