Shirin gwamnatin Oyo na bude makarantu ba daidai bane - Gwamnatin Tarayya

Shirin gwamnatin Oyo na bude makarantu ba daidai bane - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa dangane da shawarar da gwamnatin jihar Oyo ta yanke na sake bude makarantu daga ranar Litinin, 29 ga watan Yuni.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, a ranar Litinin, ya ce shawarar da gwamnatin Oyo ta yanke na bude makarantu a wannan yanayi babban kuskure ne.

Ya yi gargadin cewa, wannan shawara da gwamnatin jihar Oyo ta yanke za ta iya janyowa a samu karuwar adadi na mutanen da cutar korona za ta harba a jihar.

Da misalin karfe 10 na ranar Litinin da daddare, jihar Oyo ce a sahu na hudu cikin jerin jihohin da suka fi kamuwa da cutar korona a duk fadin kasar kamar yadda alkaluman Cibiyar NCDC suka nuna.

Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona
Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona
Asali: Twitter

Ministan ya bayyana damuwa kwarai dangane da shirin gwamnatin Oyo na bude makarantu yayin zaman karin haske da kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona ya gudanar a Abuja.

Tuni dai gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya fitar da tsare-tsaren sake bude makarantu da nufin baiwa dalibai damar komawa aji domin su ci gaba da daukan darasi.

Sai dai haka yana cin karo da umarnin gwamnatin tarayya wadda ta bukaci makarantu su ci gaba da kasancewa a rufe a fafutikar da ta ke yi na dakile yaduwar annobar korona.

KARANTA KUMA: Mutane 6879 sun warke daga cutar korona a Najeriya - NCDC

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Nwajiuba ya ce ma'aikatar ilimi ta tarayya ba ta gindaya wasu sharuda ba na bude makarantu ga kowace gwamnatin jiha a fadin tarayya.

Da wannan ne Ministan ya ke neman gwamnoni su mike tsaye wajen sauke babban nauyin da ya rataya a wuyansu na tsare rayukan al'ummominsu.

Yayin jaddada dalilin da ya sanya ba za a iya bude makarantu ba a yanzu a wannan yanayi, ministan ya ce yin hakan zai iya jefa malamai da dalibai cikin hatsarin kamuwa da cutar korona.

Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan sassauta dokar kulle da gwamnatin jihar Oyo ta yi a makon da ya gabata, ta kuma ba da umarnin a buɗewa ɗalibai makarantu domin su koma aji wajen ci gaba da daukan darasi.

Sai dai fa gwamnatin ta fayyace cewa, ɗaliban da suke ajin karshe a kowane matakin karatu na firamare da sakandire, su ne kadai za su koma makarantu a halin yanzu.

Ta ba da umarnin cewa, ɗaliban aji shida na makarantun firamare da kuma 'yan aji uku da 'yan aji shida na makarantun sakandire su koma ajujuwansu daga ranar 29 ga watan Yuni.

Hakan ya na kunshe cikin sanarwar da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin jihar Oyo, Taiwo Adisa ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel