Yanzu: Yan majalisar dokokin jihar Imo 13 sun kamu da cutar Coronavirus
- Annobar cutar COVID-19 ta kai simame majalisar dokokin jihar Imo
- Akalla mambobin majalisar 13 sun kamu da cutar
Hankula sun tashi a jihar Imo yayinda mambobin majalisar dokokin jihar 13 suka kamu da cutar nan mai toshe numafashi wato Coronavirus, rahoton Channels TV ya bayyana.
Wannan ya bayyana ne kwanaki shida bayan dan majalisan farko ya kamu da cutar amma aka ki bayyana sunansa.
Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a jihar, Farfesa Maurice Iwu, ya bayyana ranar Talata, 16 ga Yuni cewa dan majalisan ya kamu da cutar.
Ya ce an killace dan majalisan da iyalinsa kuma an baiwa dukkan sauran mambobin majalisar umurnin suyi gwajin cutar.
Yayinda yake magana da manema labarai a birnin Owerri, Farfesa Iwu ya kara cewa wata mai jego wacce ta kamu da cutar ta mutu bayan haifan yan biyu cikin lafiya.
Bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, jimillan mutane 243 suka kamu da cutar a jihar Imo.

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng