Mafita 2 ga Musulman Najeriya da suka yi niyyar zuwa Hajji - NAHCON

Mafita 2 ga Musulman Najeriya da suka yi niyyar zuwa Hajji - NAHCON

- Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa za'ayi Hajji wannan shekarar duk da barazanar COVID-19

- Amma Hajjin bana zai gudana ne ba tare da baki daga kasashen duniya ba, mazauna kasar kadai zasuyi

- Maniyyatan Najeriya da dama sun biya wani kason kudin tafiya Hajji gabanin sanarwan

Sakamakon sanarwar da gwamnatin kasar Saudiyya tayi ranar Litinin cewa mazauna kasar kadai zasu yi aikin Hajjin bana, zabi biyu kadai ya ragewa maniyyatan Najeriya.

Shugaban hukumar jin dadin alhazai, NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyanawa Daily Trust a sakon waya cewa mafita yanzu shine imma a mayar musu da kudadensu ko kuma su bar kudin sai Hajjin shekara mai zuwa.

Yace: "Sakonmu ga maniyyata shine suna da mafita biyu: Su karbi kudaden da suka biya ko kuma su bar kudin madadin Hajjin badi."

Kamfanin sufurin mahajjata sun bayyana cewa tuni sun rungumi kaddara bisa hukuncin da hukumomin kasar Saudiyya suka yanke.

Mafita 2 ga Musulman Najeriya da suka yi niyyar zuwa Hajji - NAHCON
Mafita 2 ga Musulman Najeriya da suka yi niyyar zuwa Hajji - NAHCON
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta hana Obaseki takara a zaben fidda gwanin PDP

A jiya mun kawo rahoton cewa Gwamnatin kasar Saudiyya ta yanke shawarar gudanar da aikin Hajji wannan shekarar amma da kayyadadden adadin yan kasashe daban-daban dake zaune cikin kasar yanzu, Saudi Gazette ta ruwaito.

A wani takarda da aka saki ranar Litinin, ma'aikatar Hajj da Umrah tace: "Dubi ga yadda annobar Coronavirus ke cigaba da gudana da kuma hadarin yaduwar cutar a wuri mai tarin jama'a, an yanke shawarar gudanar da hajjin wannan shekarar (1441 H/ 2020 AD) da kayyadaddun maniyyata yan kasashe daban-daban dake zaune a Saudiyya yanzu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel