Da duminsa: Kotu ta hana Obaseki takara a zaben fidda gwanin PDP

Da duminsa: Kotu ta hana Obaseki takara a zaben fidda gwanin PDP

- Da alamun gwamnan jihar Edo ya fara fuskantar mishkila a sabuwar jam'iyyar da ya shiga

- Wata babbar kotun tarayya ta dakatad da gwamnan daga takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP

- Wannan ya biyo bayan fitarsa daga jam'iyyar APC inda akace bai cancanci takara ba

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Port Harcourt, jihar Rivers ta dakatad da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, daga musharaka a zaben fidda gwanin dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), rahoton SH ya bayyana haka.

Obaseki ya sauya sheka jam'iyyar PDP ne bayan kwamitin tantancewar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta ce bai cancanci takara karkashinta ba.

Daga bisani, shi da mataimakinsa Philip Shaibu suka sauya sheka PDP kuma aka basu daman takara kuma aka tantancesu.

Amma daya daga cikin yan takara a jam'iyyar PDP, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya shigar da kara kotu cewa a hana gwamnan takara a zaben fidda gwanin da aka shirya yi ranar Alhamis, 25 ga Yuni.

A karar da ya shigar, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya ce yan takaran da suka sayi Fom kuma aka tantance lokacin da aka kayyade tun farko ya kamata a amince suyi musharaka a zaben fidda gwanin.

Hakazalika ya tuhumci sihhancin takardun karatun Obaseki; babban dalilin da ya sa jam'iyyar APC ta hana shi takara.

D aduminsa: Kotu ta hana Obaseki takara a zaben fidda gwanin PDP
D aduminsa: Kotu ta hana Obaseki takara a zaben fidda gwanin PDP
Asali: UGC

A shari'ar da ya yanke ranar Litinin, Alkali E.A Obile ya amince da bukatar Omoregie Ogbeide-Ihama.

Saboda haka, Alkalin ya umurci hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC kada tayi lissafi da gwamnan har sai an yanke hukuncin karshe kan lamarin.

Ya dage karar zuwa ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2020.

A ranar Litinin, mutumin da yayi takarar gwamnan jihar Edo karkashin PDP a 2016 Osagie Ize-Iyamu, ne ya lashe zaben fidda gwanin dan takara a jam'iyyar APC.

Za'a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo ranar asabar, 19 ga watan Satumba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel