A jihar Katsina za ayi bikin ranar Sojojin Najeriya na bana

A jihar Katsina za ayi bikin ranar Sojojin Najeriya na bana

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Litinin ta sanar da cewa bikin ranar sojoji na bana za ayi shi ne a jihar Katsina don kaddamar da wani atisaye mai lakabin “Ex Sahel Sanity” da nufin magance 'yan bindiga da ke arewa maso yamma.

Mai magana da yawun rundunar, Kwanel Sagir Musa, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa wannan na daga cikin matakan da aka dauka yayin taron manyan jami'an rundunar.

Ya ce babban hafson sojojin kasa, Laftanant Janar Tukur Buratai a ranar Litinin ya yi taro na musamman da manyan jamian rundunar da kwamandojin da ke Hedkwatar rundunar.

A jihar Katsina za ayi bikin ranar Sojoji na bana
A jihar Katsina za ayi bikin ranar Sojoji na bana.
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Musa ya ce an kira taron ne domin daukan sabbin matakai da zaburar da sojoji domin yaki da Boko Haram da ta'adanci da 'yan bindiga da ke adabar yankin arewa maso yamma da wasu kallubalen tsaron.

Ya ce an tattauna muhimman batutuwa wurin taron da ke da alaka da tsaro, yaki da ta'addanci da sauran matakan tabbatar da tsaro a tarayyar Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin taron an jadada bukatar da ke akwai ga kwamandoji, jami'ai da dakarun sojoji su rubunya kokarin da suke yi don ganin an yi maganin duk wata barazana ta tsaro a kasar.

Ya kara da cewa Buratai ya umurci dukkan kwamandoji/GOCs, jami'ai da dakarun rundunar sojojin Najeriya su tabbatar sun kara jajircewa don murkushe Boko Haram da sauran kallubalen tsaro da ke adabar kasar kamar yadda Shugaban kasa ya umurta.

Musa ya ce Buratai ya yi gargadin cewa yana son ya ga canji na gari a dukkan ayyukan da sojojin ke yi na samar da tsaro a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel