Dalilin da yasa 'yan N-Power 12,000 basu samu alawus na wata uku ba - Minista

Dalilin da yasa 'yan N-Power 12,000 basu samu alawus na wata uku ba - Minista

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta fito fili ta amince cewa akwai kimanin matasa 12,000 masu cin moriyar tsarin tallafawa matasa; wato N-Power, da basu samu alawus dinsu na wata uku ba.

Ministar jin kai da harkokin hidimtawa 'yan kasa, Sadiya Umar Farouq, ce ta tabbatar da hakan yayin taron kwamitin kar ta kwana da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar korona a fadin kasa (PTF).

A karshen makon jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta sallami matasa 500,000 da ta fara dauka a karkashin tsarin N-Power a tsakanin shekarar 2016 da 2018.

Ministar ta alakanta jinkirin biyan matasan 12,000 da tangarda a bangaren gudanar da aiki, tare da bayyana cewa ma'aikatarta ta na aiki tare da ofishin babban akawu na kasa domin warware matsalar.

"Ma'aikatarmu ta biya dukkan 'yan N-Power da aka tabbtar dasu kuma aka samu izinin biyansu, mu na da matasa 500,000.

Dalilin da yasa 'yan N-Power 12,000 basu samu alawus na wata uku ba - Minista
Minista Sadiya Umar Farouq
Asali: Facebook

"Mu na aiki tare da ofishin babban akawu na kasa domin warware matsalar wasu daga cikin matasan da basa samun alawus a karshen wata.

DUBA WANNAN: Tsohon shugaban majalisa ya sanar da yin murabus daga zama mamba a jam'iyyar APC

"Mun dan samu tangarda yayin da muke hijira daga tsohon tsarin biyan alawus zuwa sabon tsarin GIFMIS na gwamnatin tarayya.

"An dan samu tangardar aiki wacce ta haifar da jinkiri a biyan alawus din matasan, sun kai kusan 12,000.

"Ko a yau (Litinin) sai da babban sakataren ma'aikatarmu ya ziyarci ofishin akanta janar domin warware matsalar," a cewarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel