Ma'aikatan Gwamnati a jihar Oyo sun koma aiki

Ma'aikatan Gwamnati a jihar Oyo sun koma aiki

A yau Litinin, 22 ga watan Yuni, daukacin ma'aikatan gwamnati a jihar Oyo, sun koma aiki biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na sassauta dokar kulle.

Ma'aikatan jihar sun koma aiki gada-gadan bayan sun yi zaman dirshan na watanni uku sakamakon dokar hana fita da aka shimfida sanadiyar annobar korona.

Tun a ranar 27 ga watan Maris ne aka rufe sakateriyar gwamnatin jihar, a yunkuri kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar annobar korona.

Sai dai an nemi manyan ma'aikata da ke kan mataki na 17 zuwa sama su koma aiki a ranar 27 ga watan Afrilu.

Gwamnan jihar Seyi Makinde, wanda kuma ya kasance shugaban kwamitin yaki da cutar korona a jihar, ya gudanar da wata ganawa da sauran 'yan kwamitinsa a ranar 15 ga watan Yuni.

Bayan wannan zama ne fadar gwamnatin ta ba da umarnin cewa, daukacin ma'aikata su koma aiki daga ranar Litinin, 22 ga watan Yuni.

Gwamnan Oyo; Seyi Makinde
Gwamnan Oyo; Seyi Makinde
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, ma'aikata sun yi tururuwar komawa aiki a yau Litinin, inda wasunsu suka koma bakin fama tun da misalin karfe 7.00 na safiya.

Da yawa daga cikin ma'aikatan da suka koma aiki sun kiyaye dokokin hana kamuwa da cutar korona, inda aka hangi da dama sanye da takunkumin rufe fuska.

Haka zalika, ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati a kowace mashiga sun tanadi sabulai da wuraren wanke a karkashiin ruwa mai gudana da kuma sunadaran wanke hannu wato sanitizer.

KARANTA KUMA: Mutane 6879 sun warke daga cutar korona a Najeriya - NCDC

Wani ma'aikaci da ke kan mataki na goma, Mista Akin Olaitan, ya ce gwamnati ta rarraba wa ma'aikata takunkumin rufe fuska guda biyu-biyu a kowace ma'aikata yayin da suka koma aiki.

Olaitan ya yabawa gwamnatin jihar bisa tanadin takunkumin rufe fuska da sauran kayyaki na dakile yaduwar cutar korona a tsakanin ma'aikata.

Haka zalika Misis Foluke Adekunle da Eunice Adeyemi, wasu ma'aikata biyu da ke kan mataki na 9, sun yi farin cikin dawowarsu aiki bayan shafe tsawon watanni uku suna hutun dole.

Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan sassauta dokar kulle da gwamnatin jihar Oyo ta yi a makon da ya gabata, ta kuma ba da umarnin a buɗe makarantu domin ɗalibai su koma aji wajen ci gaba da daukan darasi.

Sai dai fa gwamnatin ta fayyace cewa, ɗaliban da suke ajin karshe a kowane matakin karatu na firamare da sakandire, su ne kadai za su koma makarantu a halin yanzu.

Ta ba da umarnin cewa, ɗaliban aji shida na makarantun firamare da kuma 'yan aji uku da 'yan aji shida na makarantun sakandire su koma ajujuwansu a ranar 29 ga watan Yuni.

Hakan ya na kunshe cikin sanarwar da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin jihar Oyo, Taiwo Adisa ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel