Ma'aikaci ya kashe kansa bayan batar da N150,000 ta ubangidansa a caca

Ma'aikaci ya kashe kansa bayan batar da N150,000 ta ubangidansa a caca

Wani ma'aikaci ya kashe kansa a jihar Bayelsa a makon da ya gabata bayan ya salwantar da N150,000 na uban gidansa bayan ya saka ta a caca amma sai aka yi masa kankat.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kudin ya salwanta ne a wasan yanar gizo wanda bai wuce cikin mintuna biyu ba.

Mutumin mai suna Suga ya yi amfani da cinikin da suka yi ne kaf na ranar don shiga gasar.

Wani ganau ba jiyau ba yace, "Suga wanda bai san yadda zai yi wa uban gidansa bayani ya yanke shawarar kashe kansa."

Yawan wadanda ke kashe kansu sakamakon cacar yanar gizo tun a shekarar da ta gabata ya kai mutum uku a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Butswat ya ce, duk da 'yan sandan sun san da aukuwar lamarin, ba a kai musu rahoto ba zuwa ofishinsu.

Butswat ya ce; "DPO din ofishin 'yan sandan Bassambri Nembe ya ce ba a kai musu rahoton aukuwar lamarin ba har zuwa ofishinsu. Ya ce dai sun ji labarin aukuwar lamarin."

Ma'aikaci ya kashe kansa bayan batar da N150,000 ta ubangidansa a caca
Ma'aikaci ya kashe kansa bayan batar da N150,000 ta ubangidansa a caca. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mijina ya biya N580,000 sadakina, ya yi alkawarin ba zai tallafi dangina ba - Budurwa ta koka

A wani labari na daban, wani makiyayi mai shekaru 20 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 54 fyade a Ugwulangwu da ke karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi har ta mutu.

Laulu Isa dan asalin jihar Nasarawa y shiga hannun 'yan sanda a ranar Talata kuma ya amsa laifinsa.

A yayin zantawa da manema labarai, Isa ya ce sau daya yayi amma sai ta fadi ta mutu, jaridar The Nation ta ruwaito. Ya yi ikirarin cewa illar giya ce ta kwashesa yayi mugun aikin.

Ya kara da cewa bashi da burin yi mata fyade amma da ta zage shi bayan taki yarda da shi, sai ya haye mata.

Ya ce, "Sunana Laulu Isa daga jihar Nasarawa. Na zo aiki ne Ebonyi. Na matukar buguwa sai na ga wata mata na tafiya. Na nufeta tare da mika bukatar lalata da ita.

"Daga nan ta fara zagina, lamarin da ya fusata ni na rama. A take na fara dukanta. Na kaita kasa na hayeta. Sau daya nayi amma ta fadi ta mutu.

"Hankalina ya tashi. Ina bakin ciki, ban taba yin fyade ba. Gara in mutu. Ku yafe min."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: