Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta dakatar da Giadom

Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta dakatar da Giadom

A yayin da rikicin jam'iyyar APC ke ci gaba da daukan sabon salo, reshen jam'iyyar na jihar Ribas, ya dakatar da mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa, Mista Victor Giadom.

Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta dakatar da Giadom saboda zarginsa da aikata wasu laifuffuka da suka saba wa kundin tsarin jam’iyyar.

Haka na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba da shawara kan harkokin sadarwa ga shugaban jam'iyyar reshen jihar, Livingstone Wechie, da ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke hukuncin dakatar da Giadom ne biyo bayan shawarwari da kwamitin bincike na jam'iyyar ya bayar.

Kwamitin ya ba da shawarar dakatar da Giadom kai tsaye daga jam'iyyar saboda laifukan da ya aikata da suka saba wa kundin tsarinta, da sanadiyar hakan ya haifar da rashin jituwa a cikinta.

Victor Giadom
Victor Giadom
Asali: UGC

Da wannan ne aka nemi Giadom ya gaggauta rubuto wasikar bai wa jam'iyyar hakuri tare da neman afuwarta. An kuma nemi ya wallafa wasikar a manyan jaridu uku na kasa.

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, rikicin jam'iyyar APC ya ci gaba da rincabewa a jihar Ribas bayan watsi da suka yi da Igo Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na jihar.

Mambobi 28 daga cikin 38 na shugabannin ne suka ki amincewa da Aguma.

Sun amince da dakatar da Aguma a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar kuma sun kafa wani kwamitin rikon kwarya wanda Sokonte Davies ya ke jagoranta.

KARANTA KUMA: Rikicin APC: Shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya saka baki

A yayin zantawa da manema labarai a garin Fatakwal da ke jihar Ribas, mambobin kwamitin sun ce Aguma na zartar da hukunci yadda ya so tare da watsi da wasikar babbar kotun da ta nada shi shugaban jam'iyyar na rikon kwarya.

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri tare da gwamnonin jam’iyyar APC a fadarsa da ke Abuja.

Wadanda suke ganawa da shugaban kasar sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da kuma gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru.

Koda dai ba a bayyana cikakken bayani kan dalilin ganawar ba, an tattaro cewa ba za ta rasa nasaba da matsalolin da suka kunno kai a cikin jam'iyyar ta su ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel