Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutum uku, sunyi garkuwa da daya

Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutum uku, sunyi garkuwa da daya

Akalla mutum uku sun rasa rayukansu a wani hari da yan bindiga suka kai a wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Dandume a Jihar Katsina ranar Litinin 22 ga watan Yunin 2020.

Yan bindigan sun kai hari kauyen Maikwama inda suka kashe mutum uku kafin suka saci shanu masu dimbin yawa kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Sun kuma sace kayan abinci.

Sun kai harin ne bayan kwana daya da kai hari wani kauye mai suna Kurmin Chakara inda suka yi garkuwa da wani Malam Kabiru.

Yan bindiga sun sake kai hari Katsina sun kashe mutum uku sunyi garkuwa da daya
Yan bindiga sun sake kai hari Katsina sun kashe mutum uku sunyi garkuwa da daya
Asali: UGC

Jihar Katsina tana fama da harin yan bindiga wanda yaki karewa.

A makon da ya wuce, fadar Shugaban kasa tayi ikirarin akwai sa hannun sarakunan gargajiya wurin hare haren da yan bindiga suke kaiwa kauyukansu.

Har yanzu muna sauraron ji ta bakin Shugaban yan sandan jihar kan batun harin.

A wani labari daban munji cewa arangama tsakanin ‘yan sa kai da ‘yan bindiga a Dajin Gwamna da ke kauyen Dan Ali na karamar hukumar Danmusa a jihar Katsaina ya kawo rashin rayuka 5, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Biyu daga cikin mamatan masu suna Abdullahi Lawal wanda aka fi sani da Kirgi da Isiya Kanawa duk ‘yan sa kai ne da ke kauyen Dan Ali.

An gano gawawwakinsu a halin yanzu amma ba a birnesu ba saboda ‘yan bindigar sun hana damar yi musu jana’iza.

Rikicin ya fara ne a washegarin da aka kashe dagacin kauyen Mazoji da ke da kusanci da su. Daga nan ne ‘yan sa kan suka hadu a kauyen Dan Ali sannan suka yanke hukuncin shiga dajin don daukar fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel