Abinda yasa gwamnatin Buhari ta batawa Trump rai - Tsohon mai bashi shawara a kan tsaro

Abinda yasa gwamnatin Buhari ta batawa Trump rai - Tsohon mai bashi shawara a kan tsaro

John Bolton, tsohon mai bawa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, shawara a kan harkokin da suka shafi tsaro, ya bayyana cewa shugaba Trump ya taba neman a dakatar da bawa Najeriya tallafin dalar Amurka $1.5bn na shekara - shekara.

Tsohon mai bayar da shawarar ya bayyana hakan ne a cikin wani littafi da ya wallafa mai taken 'a cikin dakin da abubuwan suka faru' (In the Room where It Happened).

Bolton, wanda ya bar gwamnatin Trump a cikin shekarar da ta gabata, ya ce shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta na karbar makudan kudaden tallafi daga Amurka duk shekara.

A cewar Bolton, Trump ya koka a kan cewa gwamnatin Buhari ba ta sayen kayan amfanin gona da aka noma a Amurka duk da irin makudan kudaden tallafi da Amurka ke bawa gwamnatin Najeriya.

Kazalika, Bolton ya bayyana cewa shugaba Trump ya nemi a rage kudaden da Amurka ke kashewa wajen tafiyar da al'amuran wasu manyan kungiyoyin kasa da kasa tare da bayar da umarnin fitar da kudi domin gina ganuwa tsakanin kasar Amurka da kasar Mexico.

A makon jiya ne Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi Alla - wadai da yawaitar kisan fararen hula a Najeriya, musamman a cikin 'yan makonnin baya bayan nan.

Abinda yasa gwamnatin Buhari ta batawa Trump rai - Tsohon mai bashi shawara a kan tsaro
Buhari da Trump
Asali: UGC

A cikin wani jawabi da sakataren gwamnati, Michael Pompeo, ya fitar ranar Laraba, 17 ga watan Yuni, 2020, kasar Amurka ta ja hankalin gwamnatin Najeriya a kan kisan fararen hula da 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a jihohin Katsina da Borno.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta haramta goyo a babur, ta bayyana dalili

"Mun yi Alla - wadai da wadannan kashe - kashe marasa dalili da babu wata manufa a cikinsu.

"A 'yan makonnin baya bayan nan, mayakan kungiyar ISIS a yankin Afrika ta yamma sun kai hare - hare tare da kashe fararen hula fiye da 120; da suka hada da mata da kananan yara, a jihar Borno.

"A ranar 9 ga watan Yuni, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani kauye a Katsina tare da kashen dumbin mutane.

"Wadannan kashe - kashe sun biyo bayan harbe wani Fasto da matarsa mai juna biyu a ranar 1 ga watan Yuni da kisan wani Limami, Dagachi, da dumbin fararen hula a ranar 5 ga watan Yuni a wani rikicin kabilanci da ya barke a jihar Taraba," a cewar Pampeo.

Gwamnatin kasar Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kara kokarinta na kare rayukan jama'a ta hanyar kawo karshen aiyukan ta'addanci tare da hukunta 'yan ta'adda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel