Likitoci za su janye yajin aiki bayan ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) za ta tsoma baki cikin rashin jituwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar Manyan Likitocin Najeriya NARD da har ta kai ga shigarsu yajin aiki.
Shugaban sashen hulda da al'umma na kungiyar gwamnonin, Abdulrazaque Bello-Barkindo, shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.
A sanarwar da Barkindo ya fitar, ya ce kungiyar gwamnonin ta gana da fusatattun Likitocin, sun kuma yanke shawarar sanya amincinsu a hannunta domin sulhunta lamarin.
Likitocin yayin bayyana fushinsu ga kungiyar gwamnonin, sun kuma ba da tabbacin za su janye aikin da suka shiga da zarar an cimma wata matsaya mai karfi.
An ruwaito cewa, dukkanin manyan kungiyar likitocin ta NARD sun hallara a sakateriyar NGF inda suka gana da shugaban NGF, Kayode Fayemi, wanda ya kasance gwamnan jihar Ekiti.

Asali: Twitter
Daga bisani kungiyar likitocin a gaban Darakta Janar na NGF, Asinshana Bayo Okauru, sun kuma gana da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, inda shi ma suka bayyana masa fushinsu.
Wannan shi ne karo na farko da kungiyar likitocin ta kai kukanta har gaban kungiyar gwamnonin kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.
Gwamna Fayemi ya yaba ma likitocin kan yadda suka ci gaba da zama a kasarsu domin yin hidima duk da tarin alheri da kuma tayin da suke samu daga kasashen waje.
KARANTA KUMA: Kasashe 10 mafi zaman lafiya a nahiyar Afrika
Sai dai Gwamnan ya tunatar da su cewa tserewa daga kasarsu ba tare da yi mata hidima ba zai zama butulci ga gwamnatin kasar da ta yi ruwa da tsaki wajen ganin sun kware a kan aikinsu.
Fayemi ya yi kira ga NARD da ta janye yajin aikin yana mai alƙawarin cewa kungiyarsu zata iyaka bakin kokarinta wajen sulhunta lamarin cikin sati ɗaya.
Ya tabbatar musu da cewa NGF za ta duba damuwar su tare da sauran mambobin ƙungiyar domin neman hanyar magance matsalolin da suka haddasa rashin jituwa tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
Likitocin wanda shugabansu ya jagoranci tawagar da ta gana da gwamnonin, Dr. Aliyu Sokomba, ya sha alwashin zai tuntubi sauran mambobin kungiyar domin su yi kirdadon kokarin da gwamnonin za su yi dangane da lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng