Karin mutum 661 sun kamu da korona a Najeriya
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 661 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.29 na daren ranar Asabar 20 ga Yuni na shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na dandalin sada zumunta na Twitter, ta ce karin karin mutune 661 da suka kamu sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Asali: Twitter
Lagos-230
Rivers-127
Delta-83
FCT-60
Oyo-51
DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege
Edo-31
Bayelsa-27
Kaduna-25
Plateau-13
Ondo-6
Nasarawa-3
Ekiti-2
Kano-2
Borno-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Asabar 20 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jumullar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 19,808.
An sallami mutum 6718 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jumullar mutum 506.
A wani labarin daban, kun ji dan majalisar jihar Enugu mai wakiltan mazabar Isa-uzo, Chijioke Ugwuwze ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Marigayin ya rasu ne sakamakon bugun zuciya kamar yadda kaninsa, Ejike ya tabbatar a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2020 kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Dan uwan marigayin ya bayyana cewa Ugwueze ya mutu yana da shekaru 49 a duniya kuma ya dade yana fama da ciwon hawan jini kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito.
Dan uwansa ya kara da cewa dan majalisar ya mutu ne a asibitin koyarwa da ke na Enugu da ke Parklane a yammacin ranar Juma'a 19 ga watan Yuni.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng