APC ta zabi Worgu Boms ya maye gurbin Giadom

APC ta zabi Worgu Boms ya maye gurbin Giadom

Jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ta bayar da shawarar a nada tsohon Attoney janar na jihar, Worgu Boms ya maye gurbin sakataren jam'iyyar na kasa, Victor Giadom.

Hillar Eta, mataimakin shugaban jam'iyyar ra APC shiyasa Kudu maso Kudu ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar Asabar a Abuja.

Eta ya ce Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar, NWC, ya dade yana aiki don ganin an maye gurbin Giadom da ya yi murabus daga jam'iyyar domin zama abokin takarar gwamna a Rivers Tony Cole a zaben 2019.

Da dumi-dumi: APC ta maye gurbin Giadom da Worgu Boms
Da dumi-dumi: APC ta maye gurbin Giadom da Worgu Boms. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Rikicin jam'iyyar ya hana Cole da abokin takararsa shiga zaben a fafata da su.

A yayin jawabin da ya yi, Eta yace an aika da sunan Bom bayan NWC da bukaci shiyar Kudu maso Kudu ta tura sunan wanda zai maye gurbin Gaidom.

"Kamar yadda ku ka sani a ranar Juma'a kotu da zartar da cewa Cif Victor Giadom ba mamba bane na NWC kuma ya dena gabatar da kansa a matsayin mamba," in ji shi.

"Tun da farko kwamitin gudanarwa ta jam'iyya ta bukaci shiyar Kudu maso Kudu na jam'iyyar da nake shugabanci ta mika sunan wanda zai maye gurbin da aka samu sakamakon murabus din da yi don takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar mu a Rivers.

"Ina son sanar da duniya cewa na karbi sunan dan jam'iyyar mu daga jihar Rivers don maye gurbin kuma shine Worgus Boms Esq, tsohon attoney janar na jihar Rivers.

"An mika sunansa ga ofishina kuma in son sanar da ku cewa kwamitin zartarwa na shiyar kudu maso kudu za ta zauna don tabbatar da sunan kuma ta mika shi ga NWC na jam'iyyar mu."

Gaidom ya nada kansa shugaban jam'iyyar APC na riko a lokacin da kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja da tabbatar da dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel