Covid-19: Mai korona daya tak ya rage a Jigawa, sauran 316 sun warke

Covid-19: Mai korona daya tak ya rage a Jigawa, sauran 316 sun warke

Gwamnatin Jigawa a ranar Asabar ta ce a halin yanzu majinyaci daya tak ta ke da shi a cibiyar killace masu korona bayan majinyata 316 sun warke sarai an kuma sallame su.

Gwamna Badaru Abubakar ne ya tabbatar da hakan a yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a gidan gwamnati da ke babban birnin jihar, Dutse kamar yadda mashawarcin gwamnan na musamman kan sabuwar kafar watsa labarai, Auwal D Sankara ya fitar.

Badaru ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta bude iyakokinta da jihohin da ta ke makwabtaka da su da suka hada da Kano, Bauchi, Katsina da Yobe.

Covid-19: Jigawa ta yi galaba kan korona, ta bude iyakokinta da Kano, Bauchi, Katsina da Yobe
Covid-19: Jigawa ta yi galaba kan korona, ta bude iyakokinta da Kano, Bauchi, Katsina da Yobe. Hoto daga gwamnatin jihar Jigawa
Asali: UGC

Kamar yadda alkalluman Hukumar Kiyayye Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC ta fitar daren Juma'a ya nuna, jumullar wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus a jihar Jigawa ya kai 317 yayin da cutar ta kashe mutum 9.

Covid-19: Mai korona daya tak ya rage a Jigawa, sauran 316 sun warke
Covid-19: Mai korona daya tak ya rage a Jigawa, sauran 316 sun warke. Hoto daga gwamnatin Jigawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Gwamnan ya ce, "Ya ku 'yan uwa na 'yan jihar Jigawa, ina farin cikin sanar da ku cewa matakan da muke dauka na yaki da Covid-19 na cigaba da samar da sakamako mai kyau."

Ya kuma sanar da cewa za a rufe cibiyar killace masu coronavirus na Fanisau "har zuwa lokacin da muka samu sabbin masu cutar da suka fi karfin ainihin cibiyar killacewar mu."

A wani labarin daban, kun ji dan majalisar jihar Enugu mai wakiltan mazabar Isa-uzo, Chijioke Ugwuwze ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Marigayin ya rasu ne sakamakon bugun zuciya kamar yadda kaninsa, Ejike ya tabbatar a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2020 kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Dan uwan marigayin ya bayyana cewa Ugwueze ya mutu yana da shekaru 49 a duniya kuma ya dade yana fama da ciwon hawan jini kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito.

Dan uwansa ya kara da cewa dan majalisar ya mutu ne a asibitin koyarwa da ke na Enugu da ke Parklane a yammacin ranar Juma'a 19 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel