Kasar Saudiyya ta janye dokar hana fita gaba daya

Kasar Saudiyya ta janye dokar hana fita gaba daya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta janye dokar hana fitan da aka sanya a fadin kasar daga ranar Lahadi, 21 ga Yuni kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta sanar ranar Asabar, Saudi Gazette ta ruwaito.

An dage dokar ne a dukkan jihohi, wanda ya hada da Makkah da Jiiddah da tun a baya aka sassauta dokar.

Ma'aikatar ta ce an amince dukkan kasuwanni su bude da sharadin za su bi dokokin kare kai da aka gindaya.

Hakazalika, ma'aikatar raya karkara da birane na kasar Saudiyya ya ce an amince shagunan aski da gyaran kan mata su bude.

Ma'aikatar ta jaddada cewa wajibi ne mutane su rika baiwa juna tazara, su sanya takunkumin fuska kuma ba'a amince mutane fiye da 50 su taru a wuri daya ba.

Bugu da kari, ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta bayyana cewa har yanzu an dakatad da aikin Umrah da Hajji kuma dukkan iyakokin kasar na kulle har yanzu.

Har yanzu dai babu tabbacin za'a gudanar da hajjin bana saboda har yanzu ana samun karuwar cutar a Masarautar Saudiyya.

A ranar Asabar, sabbin mutane 3,941 suka kamu da cutar kamar yadda Alkaluman ma'aikatar lafiya kasar ya bayyana.

Kawo yanzu, alkaluman ma'aikatar lafiya ya ce mutane 154,233 suka kamu da cutar Coronavirus a kasar Saudiyya. Yayinda 98,917 suka samu waraka, 1,230 sun rigamu gidan gaskiya

KU KARANTA: Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutane 7

Kasar Saudiyya ta janye dokar hana a fita gaba daya
Kasar Saudiyya ta janye dokar hana a fita gaba daya
Asali: UGC

Legit Hausa ta kawo muku labarin cewa za'a bude kimanin Masallatai 1,560, manya da kanana, fari daga Sallar Asuban ranar Lahadi, bayan kwanaki 90 da rufewa domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a kasar Saudiyya, Saudi Gazzete ta rahoto.

Ma'aikatar lamuran addinin Musulunci dake birnin Makkah ta shirya dukkan Masallatan bisa ka'idojin da aka gindaya.

Daga cikin ka'idojin shine samar da taburman Sallah na musamman mai amfani sau daya, da kuma bayar da tazara a cikin sahu.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki 20 da bude Masallacin Madina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel