Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole

Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole

Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a gunduma ta 10 na karamar hukumar Etsako ta yamma a jihar Edo sun sanar dage dakatarwan da suka yiwa kwamred Adams Oshiomole matsayin mamban jam'iyyar.

Yayin hira da manema labarai a Abuja, Emuakemeh Sule, wanda shine sakataren guduman ya ce mambobi 17 cikin 26 sun rattafa hannun kan haka, Ledaership ta ruwaito.

Legit ta ruwaito cewa an dakatad da kwamred Oshiomole ne daga jam'iyyar a watan Nuwamba 2019 bayan rikicin ya kaure tsakaninsa da Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo.

Bayan haka wata kotu dake zamanta a Abuja ta dakatad da shi daga kujerar shugaba inda tace ba zai yiwu ya cigaba da zama shugaban uwar jam'iyyar ba tun da an koreshi daga jam'iyyar a gundumarsa.

A ranar 4 ga watan Maris ne kotun ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.

A ranar 16 ga Yuni kuwa, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Alkalan kotun da suka samu jagorancin shugaban alkalan kotun daukaka kara, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem sun yanke hukuncin cewa daukaka karar Oshiomhole bata da tushe.

Hakan ya faru ne a ranar da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fita daga jam'iyyar APC bayan ganawarsa da Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole
Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan sayen fam, Obaseki ya dira hedkwatar PDP domin a tantanceshi

Daga ranar aka shika rikici a jam'iyyar inda mutane biyu suka dane kujerar Oshiomole matsayin shugaban jam'iyyar na riko.

Yayinda kwamitin gudanarwa NWC ta alanta mataimakin shugaban jam'iyyar (yankin kudu), Abiola Ajimobi, matsayin mukaddashin shugaba, mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom, ya ce shine sahihin mukaddashin shugaban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel