Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutane 7

Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutane 7

Akalla mutane bakwai (7) sun rasa rayukansu bayan mumunan harin da yan bindiga suka kai kauyukan Kasai da Nahuta a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.

Wani mazaunin Kurmiyal, garin da ke kusa da inda aka kai hari, Sama'ila Lihidda, ya tabbatar da hakan da wakilan Channels TV ranar Asabar.

Lihidda ya jaddada cewa yan ta'addan sun farwa garin ne a daren jiya misalin karfe 7 yayinda mazauna ke shirin Sallar Magariba.

Duk da cewa hukumar yan sanda bata tabbatar da harin ba,, Sama'ila Lihidda yace "a garin Kasai kadai an kashe mutane biyu kuma a garin Nahuta an kashe biyar yayinda da dama sun jikkata."

"Yayinda suka dia kan babura, yan bindigan rike da bindigogi suka fara harbin kan mai uwa da wabi domin fitittikan mutane.."

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda, SP Gambo Isah, ya ce bai da masaniya amma zai tuntubi na kusa da wajen.

Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutane 7
Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutane 7
Asali: UGC

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa kan yadda lamarin tsaro ya tabarbare a kasar yan kwanakin nan

Mai bada shawara kan lamuran tsaro NSA, Manjo Janar Babagana Munguno (mai murabus), ya bayyana hakan bayan zamansu da shugaban kasan.

Munguno ya bayyanawa manema labaran fadar shugaban kasa cewa shugaban kasan ya bukaci hafsoshin tsaro su kara kaimi wajen shawo kan matsalar tsaro.

A cewarsa, shugaba Buhari yace, duk da cewa hafsoshin tsaron na iyakan kokarinsu, da alamun sun yi kasa a gwiwa wajen fuskantar matsalar tsaron da ta zaman babban kalubale.

Ya zajjarasu inda yace ba zai sake daukan uzuri ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel