Wani dan majalisar Najeriya, Ugwueze ya sake rasuwa yayin da ake fama da annobar coronavirus

Wani dan majalisar Najeriya, Ugwueze ya sake rasuwa yayin da ake fama da annobar coronavirus

- Dan majalisar jihar Enugu, Chijioke Ugwueze ya rasu

- Rahotanni sun ce Ugwueze ya rasu ne a yammacin ranar Juma'a, 19 ga watan Yuni

- Iyalan dan majalisar sun ce bugun zuciya ne ta yi sanadin mutuwarsa

Dan majalisar jihar Enugu mai wakiltan mazabar Isa-uzo, Chijioke Ugwuwze ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Marigayin ya rasu ne sakamakon bugun zuciya kamar yadda kaninsa, Ejike ya tabbatar a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2020 kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Dan uwan marigayin ya bayyana cewa Ugwueze ya mutu yana da shekaru 49 a duniya kuma ya dade yana fama da ciwon hawan jini kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito.

Allah ya sake yi wa wani dan majalisa a Najeriya rasuwa
Allah ya sake yi wa wani dan majalisa a Najeriya rasuwa
Asali: UGC

Dan uwansa ya kara da cewa dan majalisar ya mutu ne a asibitin koyarwa da ke na Enugu da ke Parklane a yammacin ranar Juma'a 19 ga watan Yuni.

DUBA WANNAN: APC na shirin dakatar da hadimin Buhari, Sanata Ojudu

A wani labarin, kun ji cewa an yankewa wani bugaggen biri dan giya hukuncin daurin rai da rai sakamakon dabi'ar rigima da ya bayyana bayan an hana shi 'abun sha' a kasar India.

Bugaggen birin mai suna Kalua ya fada cikin mutum 250 inda ya tarwatsa su tare da kashe mutum daya har lahira.

A cikin wannan makon, masu kula da gidan namun daji da ke Kanpur sun tabbatar da cewa birin babban hatsari ne ga sauran 'yan uwansa kuma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Birin da ya saba shan giyar mallakar wani likitan ido ne da ke yankin Mirzapur mai suna Uttar Pradesh, wanda makwabtansa suka tabbatar da cewa shi ya koya masa shan giya da cin naman birai 'yan uwansa, jaridar Daily Mail ta ruwaito.

A lokacin da aka samu gawar mamallakin birin, fusattacciyar dabbar ta fada titi inda ta dinga kaiwa da kawowa tana harar jama'a.

Birin ya dinga azabtar da mata tare da kananan yara. Kalua ya ruda masu tsaron namun daji da ke Mirzapur amma da kyar suka kama shi daga bisani, IANS ta ruwaito.

A halin yanzu, shekarun Kalua 6 kuma an mika sa gidan namun daji da ke Kanpur inda baya saurarawa dabbobi ballantana birai.

"Mun ajiyeshi na watanni a killace kafin mu sauya masa keji," Dr. Mohammad Nasir ya sanar.

"Babu wani sauyi a halin fitinarsa. A yanzu shekarunsa uku a nan amma mun yanke hukuncin zai zauna a killace har karshen rayuwarsa," yace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel