Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege

Dakarun Sojojin Saman Najeriya, NAF, karkashin Operation Lafiya Dole sun kashe yan ta'adan kungiyar Boko Haram da dama sun kuma kwace motarsu mai dauke da bindiga.

Sojojin sun kai wannan harin ne a cibiyar tsara zirga-zirga da matattaran 'yan ta'adan da ke kan iyakar dajin Sambisa a jihar Borno kamar yadda rundunar ta sanar a shafinta na Twitter @DefenceInfoNG.

Sun kai harin ne a ranar 17 ga watan Yunin 2020 bayan yin amfani da na'urar leken asiri ta ISR da kuma tattara bayannan sirri da ya nuna mayakan kungiyar masu yawa sun taru a nan har da motarsu mai bindiga.

DUBA WANNAN: APC na shirin dakatar da hadimin Buhari, Sanata Ojudu

Bayan hakan ne rundunar ta NAF ta aike da jiragen yakin ta zuwa matattaran yan taadan don tarwatsa gine-ginen tare da kashe da dama cikin 'yan ta'adan.

Wasu daga cikin 'yan ta'adan sun yi yunkurin tserewa cikin motar mai dauke da bindigar harbo jiragen sama daga bisani suka fara fafatawa da sojojin da suka kai harin ta sama.

Sai dai bayan amfani da wasu dabarun yakin sama, jiragen na NAF sun bi motar yakin sun ragargaza ta a hanyar ta ne ficewa daga kauyen.

Yan taadan da ke cikin motar sun yi kokarin tserewa amma mayakan sojojin da ke tuka jiragen sun bi su sun musu dauki dai-dai.

Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege
Kalli bidiyon yadda sojoji suka yi wa 'yan ta'adda 'ruwan wuta' a matattaransu da ke Bula Korege. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

A wani labari na daban, jami'in dan sanda ya harbe matashi mai shekaru 20 a duniya da ke kan babur din haya bayan ya kasa bashi N100.

Mazauna yankin sun ce, sai da dan sanda ya saita matashin mai suna Arabo Dauda sannan ya sakar masa harsashi, a wurin duba matafiya da ke garin maiha.

Lamarin ya haddasa hargitsi a yankin, bayan da matasa suka fara zanga-zanga tare da barazanar kai hari ofishin 'yan sandan yankin.

Har a halin yanzu ba a samu damar zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ba, DSP Sulaiman Nguroje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel