APC na shirin dakatar da hadimin Buhari, Sanata Ojudu

APC na shirin dakatar da hadimin Buhari, Sanata Ojudu

Shugabanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ekiti za su dakatar da mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari na musamman a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu kan zargin yi wa jam'iyya zagon kasa.

An shigar da kara a kan lamarin a babban kotun birnin tarayya Abuja amma an dage sauraron shari'a zuwa ranar 6 ga watan Yulin 2020.

Daily Trust ta ruwaito cewa hadimin shugaban kasar, yayin wata hira da aka yi da shi a makon da ta gabata ya zargi gwamnan jihar, Dr Kayode Fayemi da yin sama da fadi da babakere wurin mulkar jihar.

APC tana shirin dakatar da hadimin Buhari, Ojudu
APC tana shirin dakatar da hadimin Buhari, Ojudu. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Gwamna Ayade ya nada sabbin hadimai 190

Ya ce gwamnan ya hana duk wani yunkurin kawo gyara al'amura a jam'iyyar da harkokin inganta jihar.

Har wa yau, ya yi ikirarin cewa Gwamna Fayemi bai tabuka wani abin azo a gani ba a jihar tun da aka zabe shi a shekarar 2018.

Kwakwarar majiya da ke kusanci da gunduma ta 8 a Ado Ado-Ekiti a ranar Jumaa ta bayyana cewa Kwamitin Gudanarwa (SWC) na jihar karkashin jagorancin Shugaban jam'iyyar Mr Paul Omotosho ta gayyaci jami'an gundumar su Ojudu.

Ta umurci su fara shirin dakatar da shi duk da cewa ba a bayyana gamsashen laifin da ya aikata ba.

Da aka tuntube shi a kan batun, Ojudu ya ce an sanar da shi abinda ke faruwa a ranar Jumaa cewa Kwamitin Gudanarwa na jihar ta fara shirin dakatar da shi.

Sai dai sakataren watsa labarai na jam'iyyar, Mr Ade Ajayi ya musanta cewa jam'iyyar na shirin dakatar da Ojudu, ya kuma yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar su yi watsi da zancen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel