Da duminsa: Bayan kwanaki 90, Za'a bude Masallatan birnin Makkah gobe

Da duminsa: Bayan kwanaki 90, Za'a bude Masallatan birnin Makkah gobe

Za'a bude mimanin Masallatai 1,560, manya da kanana, fari daga Sallar Asuban ranar Lahadi, bayan kwanaki 90 a rufe domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a kasar Saudiyya, Saudi Gazzete ta rahoto.

Ma'aikatar lamuran addinin Musulunci dake birnin Makkah ta shirya dukkan Masallatan bisa ka'idojin da aka gindaya.

Daga cikin ka'idojin shine samar da taburman Sallah na musamman mai amfani sau daya, da kuma bayar da tazara a cikin sahu.

Matasa da dama sun taimaKa Fisabilillah wajen shirya Masallatan domin amfanin al'ummar birnin Makkah bisa ga sharrudan da ma'aikatar lafiya kasar ta gindaya.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki 20 da bude Masallacin Madina.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Sarkin kasar Saudiyya, Malik Salman Ibn AbdulAziz ya bada umurnin bude Masallacin Manzon Allah S.A.W dake Madina fari daga ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

An fara bari mutane na shigowa amma da sharrudan kare kai daga cutar Coronavirus da ta wajabta kulle Masallaci na tsawon watanni biyu.

Ma'aikatar harkokin Masallatan Harama biyu, karkashin jagorancin Sheikh Abdurrahman Sudais, ta kammala shirye-shiryen bude Malsallacin Madina da sharadin kashi 40% na mutanen da Masallacin ta saba dauka za'a amince su shiga.

Kawo yanzu, alkaluman ma'aikatar lafiya ya ce mutane 150,292 suka kamu da cutar Coronavirus a kasar Saudiyya. Yayinda 95, 764 suka samu waraka, 1,184 sun rigamu gidan gaskiya

Da duminsa: Bayan kwanaki 90, Za'a bude Masallatan birnin Makkah gobe
Da duminsa: Bayan kwanaki 90, Za'a bude Masallatan birnin Makkah gobe
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabbin mutane 667 sun harbu da cutar Korona a Najeriya

Har yanzu dai babu tabbacin za'a gudanar da hajjin bana saboda har yanzu ana samun karuwar cutar a Masarautar Sadiyya.

A ranar Juma'a, sabbin mutane 4,301 kamar yadda Alkaluman ma'aikatar lafiya kasar ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel