Yadda matar aure ta tozarta mijinta a kasar waje bayan ta gano yana da wata mata a Najeriya

Yadda matar aure ta tozarta mijinta a kasar waje bayan ta gano yana da wata mata a Najeriya

Wata mawakiyar Najeriya da ke zama a kasar waje ta fallasa mijinta a shafinta na Facebook bayan ta gano cewa yana da iyali a Najeriya amma ya boye mata don samun takardun zama a kasar.

A bidiyon, Osemwengie Rejoice wacce aka fi sani da Young Mummy, an ga tana hana mijinta shiga gidanta. Ta sanar da masu kallo cewa ya yi karyar yana sonta saboda yana son takardun zama a kasar. A haka ya dirka mata ciki sannan ya dawo gidanta.

Osemwengie Rejoice ta ce ya fara cin zarafinta bayan sun tare. Yana dukanta a gidanta amma bata sanar da dalilin dukan ba.

Ta kara da cewa, a koda yaushe baya son ganinta da mutane, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

"Idan ina yi wa 'yar uwata magana, sai mu fara fada. Ko wasu mutane na daban nake yi wa magana baya barina," ta bayyana.

Ta bayyana cewa, ta tambayeshi ko yana da iyali kafin su fara soyayya amma sai ya musanta.

A bidiyon, ta bukaceshi da ya bar mata gidanta ko ta kira 'yan sanda. Shi kuwa ya gurfana a gabanta yana rokonta ganin cewa bashi da wurin zuwa.

KU KARANTA: Mijina ya biya N580,000 sadakina, ya yi alkawarin ba zai tallafi dangina ba - Budurwa ta koka

A wani labari na daban, bayan majalisar dinkin duniya ta ware ranar 19 ga watan Yunin duk shekara don yaki da cin zarafi, wata baiwar Allah da ta bukaci a boye sunanta ta shaida wa BBC cewa "'yan Boko Haram sun ci zarafinmu inda suka dinga lalata da mu."

Matashiyar ta sanar da cewa wannan lamarin ya auku ne a lokacin da mayakan ta'addancin Boko Haram suka kai hari garinsu.

A cewarta, "Mayakan sun shigo garinmu a ranar wata Talata suna kabbara har suka karbe garin. Sun kashe dukkan maza sannan suka kada matan."

Ta kara da cewa "ranar wata Talata sai 'yan Boko Haram suka shigo garinmu suna kabbara inda suka karbe garin suka kuma kashe duk maza sannan sai suka kada duk mata zuwa daji bayan sun kone garin.

"A wannan ranar kawuna ya zo wanda kanin mahaifina ne, ya ce in bishi na zama ganimar yaki. Daga nan ya tafi dani ya dinga saduwa da ni."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel