Edo 2020: A karo na biyu, PDP ta sake dage ranar zaben fidda gwani

Edo 2020: A karo na biyu, PDP ta sake dage ranar zaben fidda gwani

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dage ranar da za ta gudanar da zaben fidda gwani na 'yan takarar gwamna a jihar Edo a karo na biyu cikin awa 24.

A ranar Alhamis, jam'iyyar ta sanar da cewa ta dage zaben da aka shirya yi a ranar 19 ga watan Yuni zuwa ranar 23 ga watan Yuni kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Amma cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, Kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce an dage zaben fidda gwanin zuwa ranar 25 ga watan Yuni.

Edo 2020: A karo na biyu, PDP ta sake dage ranar zaben fidda gwani
Edo 2020: A karo na biyu, PDP ta sake dage ranar zaben fidda gwani. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Edo 2020: Dalilin da yasa zan yi takara karkashin PDP - Obaseki

Sanarwar ta ce, "Kwamitin Gudanarwa, NWC, na jam'iyyar Peoples Democratic Party ta bawa Gwamnan Edo Godwin Obaseki dama ta musamman na shigar takarar zaben fidda gwani."

"Matakin da NWC din suka dauka ya dace da sashi na 29(2)(b) na kundin tsarin mulkin PDP da ya bawa NEC ikon aikata hakan a sashi na (50)(3)(b) a kundin tsarin mulkin.

"NWC ta yi amfani da ikon da ta ke da shi wurin amsar uzurin da jamian mazaba, karamar hukuma da jihar Edo na jamiyyar suka gabatar kuma ta bawa Mai girma, Gwamna Godwin Obaseki daman shiga takarar zaben fidda gwani na kujerar gwamna a PDP.

"Kazalika, NWC ta kuma dage zaben fidda gwani na gwamnan Edo da a baya aka shirya yi a ranar Talata 23 ga watan Yuni zuwa ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2020."

An fitar da wannan sanarwar ne awanni bayan an bawa Gwamna Godwin Obaseki damar shiga takarar zaben fidda gwani na jamiyyar ta PDP.

Obaseki, wanda ya lashe zabe a karkashin jamiyyar All Progressives Congress (APC), ya koma PDP ne bayan an hana shi shiga takarar gwamna a karkashin jamiyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel