Tsugunnu bata kare ba: Matsaloli 5 dake gaban Godwin Obaseki

Tsugunnu bata kare ba: Matsaloli 5 dake gaban Godwin Obaseki

Kamar yadda akayi hasashe, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya koma jam'iyyar PDP ranar Juma'a. Ya ce zai yi takaran kujeran gwamna karkashin jam'iyyar.

Amma tsugunnu bata kare ba, akwai sauran gadoji biyar da yake bukatan tsallakewa kafin ya cimma manufarsa na zarcewa a kujerarsa na gwamna.

Ga jerin yakoka biyar da ya wajaba Obaseki ya ci kafin ya iya zarcewa:

1. Amincewar PDP da shi: Ko kafin zuwansa, jam'iyyar PDP na da karfi a jihar Edo. A yanzu haka PDP ke rike da kujerun Sanatoci 2 cikin 3 na jihar.

Akwai wadanda basu ji dadin zuwan Obaseki jam'iyyar ba. Akwai wadanda suke ganin sun yiwa jam'iyyar bauta amma ana kokarin baiwa wani mulki a sama. Akwai sauran yaki gabansa.

2. Tikitin takara: Duk da cewa jam'iyyar ta amince yayi takara karkashinta, ta bayyana mai karara cewa ba zata bashi tikitin kai tsaye ba. Wajibi ne yayi takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar.

Shin zai iya kara samun nasara kan wadanda ya samu a cikin gida?

3. Salon zaben da PDP ta zaba: Kamar yadda INEC ta wallafa, jam'iyyar PDP ta zabi amfani da salon Deleget wajen fidda gwanin yan takara.

Sananne abu ne a siyasar Najeriya cewa salon zaben Deleget, wasu yan sanannun yan tsiraru ne zasu yi zabe. Shin Obaseki zai iya shawo kansu cikin dan kankanin lokacin da ya rage? Shin sauran yan takaran uku da aka tantance zasu bari ya zarce musu?

Tsugunnu bata kare ba: Matsaloli 5 dake gaban Godwin Obaseki
Tsugunnu bata kare ba: Matsaloli 5 dake gaban Godwin Obaseki
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin shugabancin APC: Victor Giadom ya aikawa hukumar INEC wasika cewa shine shugaban jam'iyyar

4. Abokin takara: Idan Obaseki ya tsallake matakin zaben fidda gwani, Shin wa zai zame mai abokin takara kujerar mataimaki?

Tuni wasu a cikin jam'iyyar PDP sun bayyana rashin amincewa Obaseki ya yi takara da mataimakinsa Philip Shaibu. Sun ce lallai wanda zai zama mataimaki ya fito daga cikinsu saboda ba zasu yi shuka ba wani ya zo ya girba.

Shin Obaseki zai ajiye mataimakin da ya tsaya dashi cikin rintsi? Shin mataimakin ba zai ga ya yaudareshi ba?

5. Zaben karshe: Idan Obaseki ya tsallake dukkan wadannan rijiyoyin kuma ya shirya karawa da APC a zaben karshe, shin zai iya kada jam'iyyar APC?

Shin kuke ganin zata kaure?

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel