Rikicin shugabancin APC: Victor Giadom ya aikawa hukumar INEC wasika cewa shine shugaban jam'iyyar

Rikicin shugabancin APC: Victor Giadom ya aikawa hukumar INEC wasika cewa shine shugaban jam'iyyar

Mataimakin sakataren jam'iyyar All Progressives Congress APC wanda ya alanta kansa shugaba ya aikewa hukumar zabe INEC wasikar cewa kotu ta nadashi jagoran jam'iyyar.

A wasika mai ranar wata 18 ga Yuni, 2020, da kuma lamba APC/NHDQ/INEC/19/020/014, Giadom ya fadawa INEC cewa daga yanzu duk wasikun da take bukata aikawa jam'iyyar su shigo ta hannunsa.

Wani sashen wasikar yace, "Cikin girmamawa ina son sanar da ku cewa an nada ni mukaddashin shugaban jam'iyyar APC."

"Gashi na jingina muku takardar hukuncin babban kotun birnin tarayya, Abuja da ta tabbatar da mulki na matsayin shugaban jam'iyyar APC."

"Ku sani cewa kotun Abuja ta dakatad da kwamred Adams Oshiomole daga kujerarsa ranar 4 ga Maris, 2020 kuma kotun daukaka kara ta tabbatar ranar 16 ga Yuni, 2020."

"A matsayi na na shugaban jam'iyyar, dukkan takardu, wasiku, da bukatu dangane da jam'iyyar APC su shigo hannu na."

Rikicin shugabancin APC: Victor Giadom ya aikawa hukumar INEC wasika cewa shine shugaban jam'iyyar
Victor Giadom
Asali: UGC

Za ku tuna cewa kotun birnin tarayya a ranar Alhamis ta tsawaita hukuncin baiwa Victor Giadom damar danewa gujerar shugaban jam'iyyar APC na kwanaki 14.

A bangare guda kuma, Prince Hilliard Eta wanda kwamitin gudanarwan jam'iyyar ta ba rikon kwaryan shugabancin jam'iyyar ya ce Idan har ana so a ga karshen rigimar cikin gidan jam’iyyar APC na din-din-din, dole majalisar koli ta NEC ta kira taro na musamman.

Hilliard Eta ya bayyana wannan bayan ya dare kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa a madadin sanata Abiola Ajimobi wanda har yanzu ya na kwance ya na fama da rashin lafiya.

Mista Prince Hilliard Eta ya ce: “Ita (NEC) ta na iya kawo karshen duk wadannan matsalolin da ake samu, idan har ana neman mafita da za ta wanye, ya zama dole mu kira taron NEC.”

Ina tunanin abin da ya hana NEC zama a cikin ‘yan kwanakin bayan nan ita ce annobar cutar COVID-19, wanda ta hana kayyadadun mutane su zauna a wuri guda."

"Ku sani cewa mu na da mutane fiye da 120 a majalisar NEC.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel